Masarautar Adamawa ta nada sababbin Hakimai a gundumomi uku na karamar hukumar Hong, biyo bayan dalilan mutuwa da tsofaffin hakiman yankin suka yi.
Zaben Hakiman wanda ya gudana a sakatariyar karamar hukumar Hong, gundumomin sun hada da Hildi da Uba da Gaya, da ke karamar hukumar ta Hong.
- Samar Da Tsaro: Ribadu Ya Yaba Wa Sarakunan Gargajiya A Adamawa
- Gwamnatin Adamawa Ta Rantsar Da Sabbin Kantamomin Raya Karkara 50
An dai gudanar da zaben cike gurbin bisa gaskiya da adalci tare da sa’ido da kulawar Galadima Adamawa, Alhaji Mustapha Aminu, wanda ya wakilci Mai Martaba Lamido Adamawa, Alhaji Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha.
Sabbin Hakiman da su ka samu nasara a zaben sun hada da Abubakar Yusuf Hakimin Hildi, Suleiman Yahaya, Uba, da Adamu Suleiman Hakimin Gaya.
Da yake jawabi ga wadanda su ka samu nasarar zama sabbin Hakiman, Galadima Adamawa Mustapha Aminu, ya shawarce su da su kasance masu jajircewa, aminci da adalci wajen sauke nauyin da aka dora mu su.
Ya kuma tunatar da su manufofi da kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da zaman lafiya, ya ce su tabbata sun yi amfani da matsayin da su ka samu wajan taka muhimmiyar rawar tabbatarwa da samar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar da suke shugabanta.
Da shima ke jawabi a taron shugaban karamar hukumar Hong Usman Innuwa Wa’aganda, ya ta ya sabbin zababbun hakiman murna, ya yaba wadanda su ka sha kaye a zaben da yadda su ka rungumi kaddara, ya ce sun cancanci a yaba mu su.
A nasa jawabin, Amadadin sababbin Hakiman, Hakimin Hildi Abubakar Yusuf, ya godewa majalisar masarautu, gwamnatin jihar, da karamar hukumar Hong bisa wannan dama da aka ba su, ya kuma ba da tabbacin cewa za su rike Amana kamar yadda aka amince mu su.
Manyan baki da dama da su ka halarci taron sun hada da Wali Adamawa, Alhaji Aminu Abdulkadir, Wakili Alkalai, Mai shari’a Nathan Musa, Madawaki Adamawa, Usman Marafa, shugabannin bangarorin tsaro na karamar hukumar Hong.