Tsohon dan wasan tsakiyar Barcelona da kasar Argentina, Javier Mascherano na shirin zama sabon kocin Inter Miami FC ta kasar Amurka.
Wannan yana nufin Mascherano zai samu damar horar da tsohon abokin wasansa na Argentina, Lionel Messi, a kulob din dake buga Major League Soccer, MLS babbar gasar kwallon kafa a kasar Amurka.
- Yawan Kudin Cinikin Shige Da Fice Na Sin Daga Watan Janairu Zuwa Oktoba Ya Karu Da Kashi 5.2%Â
- Wasu Gwamnonin Da Ake Hasashen Ba Za Su Koma Kan Kujerunsu Ba A 2027
Babban dan jarida kuma masanin harkar kwallon kafa, Fabrizio Romano ne, ya bayyana hakan cikin wani sakon da ya dora a shafinsa na X a ranar Juma’a.
Javier Mascherano zai zama sabon kocin Inter Miami, kamar yadda yarjejeniyar da aka sanya wa hannu ta nuna inda zai sake hadewa da tsoffin abokan wasansa a Barcelona Lionel Messi, Sergio Bosquets, Luis Suarez da Jordi Alba.
Mascherano zai maye gurbin Gerardo Tata Martino, wanda kwanan nan ya bar mukaminsa na kocin Inter Miami.
Martino ya bar Inter Miami saboda dalilai na kashin kansa, yayin da ya rage shekara daya kwantiraginsa ya kare.