Ibrahim Gidado, mashawarcin Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Tambuwal, ya fice daga Jam’iyyar PDP zuwa APC.
Mai magana da yawun Sanata Aliyu Wamakko, Bashar Abubakar ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a yau lahadi inda ya kara da cewa jagoran APC a jihar ne ya karbi Ibrahim Gidado a yau lahadi.
Gidado ya shelanta cewa ya canza sheka zuwa APC ne saboda PDP reshen jihar ba ta da alkibla da kuma rashin aminci a tsakanin shugabanninta na jihar.
Gidado tsohon dan Majalisar Dokoki ne a jihar Sokoto, inda ya wakilci mazabar Sokoto ta kudu.
Ya yi kira ga Shugabanni APC a jihar da su hada karfi da karfe don a ceto jihar Daga hannun Gwamnatin PDP a jihar musamman ganin cewa Gwamnatin Tambuwal ta Gaza cika alkawuranta.
A na sa jawabin Wamakko ya yaba wa Gidado kan yanke shawar ficewa daga PDP Inda ya ba shi tabbacin cewa za a yi masa adalci a Jamiyyar APC.