Wani tsoho, Alhaji Musa Tsafe dake karamar hukumar Tsafe a jihar Zamafara, ya ki amince wa ya saki wata Jikarsa da ya aura tsawon shekaru 20.
Alhaji Musa ya yanke shawarar kin sakin jikar tasa ce mai suna Wasila Isah Tsafe ‘yar shekara 35 bayan an sanar da shi cewa auren na su haramtacce ne.
Matar tasa, Wasila Tsafe, ta haifar wa Alhaji Musa ‘ya’ya 8.
An rahoto cewa, an sanar da Masarautar Tsafe kan maganar auren, inda dattawan afadar suka yiwa Alhaji Musa kiranye, bayan gudanar da bincike aka sheda wa Alhaji Musa cewa, auren na sa da jikarsa bisa sharudan addinin musulunci haramtacce ne.
Hakazalika, Malaman addinin musulunci sun shawarci Musa ya saki Jikarsa da yake aure, Wasila Tsafe amma lamarin ya cutura ga Alhaji Musa Inda yace hakan ba za ta sabu ba.
Biyo bayan tirjiyar da Alhaji Musa ya yi, Hukumar Hisba ta karamar huíikumar Tsafe ta maka Alhaji Musa kara a gaban Babbar kotun shari’ar Musulunci dake Jihar Zamfara.
kotun ta sa ranar da 21 ga watan Yulin 2022 ranar sauraron karar.