‘Yan Nijeriya wadanda suke fama da cutar Sikari sun yi kira da gwamnatin tarayya da cewar ta cire harajin da ake biya na magunguna,da sauran kayan gwaji na cutar Sikari saboda yadda farashin magungunan ya karu ya kara sa wadanda suke fama da cutar cikin mawuyacin hali na rayuwa.
Binciken da jaridar LEADERSHIP ta gudanar ya nuna mai fama da cutar Sikari a Nijeriya yana kashe Naira dubu talatin (#30,000) kowanne wata a wannan shekara ta muke ciki ta 2022, wannan kudin magani ne da kuma gwaji,wanda idan aka tuna a baya shekarar 2019 kudin Naira dubu goma ne (#10,000) ake biya.
Kwanturola-Janar Na NIS Ya Amince Da Nadin Tony Akuneme A Matsayin Sabon Kakakin Hukumar Na Kasa
Sauya Fasalin Naira Zai Karya Darajar Dalar Amurka Zuwa Naira 200 Duk Daya – EFCC
Duk wannan ma baa bin damuwa bane matsaslar ita ce shi maganin insulin da kwararru na cutar Sikari (endocrinologist), ba samun shi ake cikin sauki ba,yayiin da su kwararrun basu da yawa.Irin hakan ke kara sa masu fama da cutar shiga wani halin kaka- nika yi.
Wata kididdigar da ba a dade da samu ba ta nuna akwai ‘yan Nijeriya milyan shida wadanda suke fama da cutar,wannan ma kamar dai shi hasashen na kwararru alkalumman sun zarce haka.Saboda kashi biyu bisa uku na masub fama da cuta a Nijeriya ba a ma gane ko su wanene ba,wannan ya kara yawan masu cutar da wahalar da suke shada kuma mace- mace sanadiyar cutar.
Duk da shan wahalar da masu fama da cutar ke yi,kwararru kan al’amarin daya shafi cutar Sikari basu da yawa a Nijeriya,domin kuwa an yi kididdigar cewar ga mutane 600,000 masu fama da cutar,kwararre daya take ne zai kula da su.
Babbar matsalar cutar a Nijeriya ita ce tana kara yaduwa yayin da maganinta yake da matsalar samu cikin sauki,idan aka yi la’akari da yadda farashin kayan gwaji da magani ke kara tashin gwauron zabo.Wannan ba a Nijeriya kadai ba har ma da sauran kasashe da suke cikin ‘yan rabbana ka wadata mu ko kuma, matsakaita wadanda kudaden da suke samu basu taka kara sun karya ba.
Duk da yake an wallafa wani rahoto kan yadda ake luar da masu fama da cutar,na wata gidauniyar yadda ake samun maganin, wanda wata kungiya ce mai zaman kanta a kasar Netherland,ta bayyana cewa ana sa ran nan da shekara ta 2030 za a samutane milyan 570 da suke fama da cutar. Yayin da kuma zuwa shekarar 2045 adadin na iya kaiwa milyan 700,
Babban jami’in gidauniyar da za a samu maganin Dakta Jayasree Iyer, ya bayyana nan da shekara ta 2045 cutar zata kar4u da milyan takwas.
Ya ce shi al’amarin da yasa kudaden kulawa da cutar suka karu abin ya wuce zamantakewa akwai ma matsalar halin rayuwar da ke ciki,inda ya kara da cewa“Kudaden da ake kashewa domin kulawa da msu cutar Sikari a Nijeriya da sauran kasashen Afirka abin ya kaidalar Amurka bilyan 12.5,wannan al’amarin kuma ya nuna gaskiyar mutane na biyan kudade masu yawa wajen magani na insulin”.
Ya ce yawan kudaden da mai fama da cutar Sikari zai kashe dala dari biyar ($500)a ko wacce shekara,wannan ba karamin abu bane musamman ma ace idan shi mara lafiyar zai biya gaba daya ko kuma wani abu daga cikin aljihunsa.
Wani kwararren dan jarida a Nijeriya, Mista. Sam Eferaro, wanda aka gano ya kamu da cutar Sikari fiye da shera goma ya bayyanawa LEADERSHIP cewa yanzu yana kashe tsakanin Naira 25,000 ko Naira 30,000 kowanne wata saboda maganin cutar Sikari, ya kara da a shekarar 2019 yana kammmala dukan abubuwan maganin kasa da Naira 10,000.
Eferaro ya ce ita tsadar ko karin kudin bai tsaya kan maganin cutar Sikari kadai ba,inda ya kara da gaba daya fashin magungunan sun karu, sai dai kuma mutane “masu fama da cutar Sikari sune suke ji a jikinsu saboda dole su cigaba da yin hakan matsawar suna son kada cutarta kara samun matsala.
“Haka take ga sauran wadanda suke fama da cututtuka kamar Hawan jini da sauran cututtuka wadanda basu saurin yaduwa.
Ya kara da cewa sauran kasashen Afirka kamar su Kamaru da Ghana suna da wasu tsare- tsare ga mutanen da suke fama da cutar Sikari,musamman ma yara.
“Babu irin wancan tsarin a Nijeriya domin gwamnatin Nijeriya bata da wani tsari ko wani kokarin da take yi na rage masu wadanda suke fama da cutar Sikari. Maimakon haka ma sai ga shi farashin magunguna da na’urar da ake bibiyar halin da mai cutar yake ciki, abin karuwa yake ko wacce shekara, saboda kudaden haraji da kuma na shigo da kaya daga kasashen waje, wadanda dole ne Kamfanonin hada magunguna suke biya domin shigo da magungunan.