Waɗanda suka yi garkuwa da tsohon shugaban hukumar masu yi wa kasa hidima ta kasa(NYSC), Birgediya-janar Maharazu Tsiga, sun bukaci a basu naira miliyan 250 a matsayin kudin fansarsa kafin su sake shi.
Daya daga cikin ‘yan uwan wanda aka yi garkuwa da shi din ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce masu garkuwar sun tuntuɓe su a ranar Alhamis da daddare, inda suka shaida musu abin da suke buƙata.
- Ƴan Bindiga Sun Kai Hari A Katsina, Sun Sace Tsohon Daraktan NYSC, Janar Tsiga
- Yadda Aka Yi Garkuwa Da Dalibai 1,591 Da ‘Yan Bautar Kasa 61 A Cikin Shekara 8
An yi garkuwa da Maharazu Tsiga ne a ranar Laraba a gidansa da ke Tsiga a karamar hukumar Bakori da ke jihar Katsina.
Masu garkuwar dai sun shiga gidan na sa da muggan makamai, inda suka ji wa mutum biyu rauni tare da kashe wani ɗan uwansu dan bindiga.
Rundunar ‘ƴansandan jihar Katsina ta tabbatar da faruwar lamarin, inda suka bayar da tabbacin cewa suna yin iya yinsu wajen ganin sun kubutar da shi.
Mai magana da yawun rundunar ‘ƴansandan jihar, Abubakar Sadiq ya ce; tuni jami’ansu sun je unguwar da gidan yake amma kafin su karasa tuni ‘ƴan bindigar sun tafi da Janar Tsigan.
Sai dai ya bayyana cewar jami’an tsaro suna aiki ba dare ba rana tare da haɗin guiwa da masu ruwa da tsaki domin kamo ‘yan bindigar.
A wani ci gaban kuma, rundunar ‘ƴansandan jihar ta Katsina ta kama wasu mutane 45 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar.