Wasu masu garkuwa da mutane domin binyan Kudin fansa, sun sako ‘yar fasto Daniel Umaru, mai shekaru 13 biyo bayan biyan kudin fansa a garin Kwarhi cikin karamar hukumar Hong a Jihar Adamawa.
Yarinyar da aka sako tana cikin mawuyacin hali, sai dai kuma ba a bayyana yawan adadin kudaden da aka biya kafin ceto rayuwarta.
Rahotanni sun tabbatar da cewa a ranar Asabar ce, aka gudanar da zana’idar ‘yan’uwan yarinyar biyu da masu garkuwa da mutanen suka kashe lokacin da suka je sace yarinyar.
Dama dai a ranar 7 ga watan Yulin 2022, wasu mutane suka shiga gidan Fasto Daniel Umaru, suna ta harbe-harben bindigogi, inda nan take suka kashe ‘ya’yansa biyu tare da yin garkuwa da ‘yarsa mai shekaru 13, yanzu haka dai Faston na ci gaba da karban magani a asibiti.
Majiya daga iyalan yarinyar sun rabbatar da cewa mutanen d suka yi garkuwa da yarinyar sun sako ta biyo bayan biyan makudan kudaden fansa, sai dai majiyar ba ta bayyana yawan kudaden ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp