Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya zabi mataimakiyar shugaban jami’ar jihar Adamawa VC. Farfesa Kelatapwa Farauta a matsayin mataimakiyarsa a zaben gwamna na 2023.
Babban daraktan yada labarai na gwamnan, Solomon Kumangar, ya tabbatar wa LEADERSHIP da hakan a wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Alhamis.
Kumangar ya ce, “An tabbatar da cewa mai girma Gwamna Ahmadu Fintiri ya zabi Farfesa Farauta a matsayin abokiyar takararsa.”
Farfesa Farauta ta fito ne daga karamar hukumar Numan ta jihar. Za ta maye gurbin Crowther Seth, daga karamar hukumar Lamurde, dukkansu daga shiyyar Sanatan Kudancin jihar suke.
Farauta ta kasance Babban Sakatariya a hukumar Ilimin bai daya ta jihar Adamawa (ADSUBEB) a shekarar 2014.
Ta kasance kwamishiniyar ilimi daga 2015-2017 sannan daga bisani aka nada ta mataimakiyar shugabar Jami’ar jihar Adamawa dake Mubi.
Ta taba zama Malama a Jami’ar Modibbo Adamawa (M.A.U) Yola.
Ta yi B.sc (Agricultural Extension) a Jami’ar Nsukka dake Inugu a shekarar 1989 kuma tana da aure da ‘ya’ya.