Masu harkar (PoS) a Nijeriya sun yi karin kudin da suke amsa da kashi fiye da 50, sun ce abinda yasa suka yi hakan, saboda suna samun karancin kudade Bankuna ne kuma suka dorawa alhakin hakan.
Yayin da bikin kirsimati da kuma hutun karshen shekara ke kara karatowa, ‘yan Nijeriya na iya shig wani halina rashin kudade, har sai idan Babban Bankin kasa wato (CBN)ya dauki matakin daya dace domin maganin lamarin.
- Rarara Bai Kawo Kudin Aurena Ba – Aisha Humaira
- Karancin Kudin Shiga Ya Jefa ‘Yan Nijeriya Miliyan 14 Cikin Kangin Talauci – Bankin Duniya
Binciken da jaridar LEADERSHIP ta yi a manyan birane kamar Abuja da Legas, ya nuna masu harkar sun yi kari a kudaden da suka amsa bayan an cire kuadde inda kudaden da suke amsa sun nunka wasu kuma dan bambancin kadan ne.Sun dora alhakin hakan ne kan wahalar da suke sha wajen samun kudin daga Bankuna da kuma ATMs.
Sai dai kuma binciken da, LEADERSHIP ta yi ya nuna cewar su masu harkar PoS suna ta kai gwauro da mari inda suke ziyartar (ATMs) saboda su kwashe kudin da aka sa masu, suna kuma yin amfani ne da katunan cire kudade daban – daban. Yawancin Bankuna suna sayar da kudaden ne ga masu harkar PoS, hakan ne yasa ‘yan Nijeriya basu da zabi illa su yi harkar da su.
Ana iya tunawa Babban Bankin kasa ya umarci Bankuna da su bada fifiko wajen sa kudi ta hanyar ATMs,da yanke hukunci mai tsanani kan Bankunan da aka samu suna aikata laifin daya karya dokar.
Duk da yake an bada umarnin masu hulda da Bankuna sun bayyana yadda karancin kudi ya kazanta a wuraren cire kudi na ATM a fadin tarayyar Nijeriya, domin kuwa abokan harkar Bankunan suna cire masu kudi mai yawa a sanadiyar sun cire kudinsu.
LEADERSHIP ta bada bayanin rashin kudade a yawancin wuraren cire kudi na ATM da ke fadin tarayyar Nijeriya.
Masu POS sun yi amfani da damar da suka samu yadda yawancin wuraren cire na ATM suka zama fankar fayau, hakan ya sa suka kara kudaden da suke amsa zuwa Naira 300 idan mutum na bukatar ya cire Naira 5000.
Sai dai kuma yawancin wuraren cire kudi na PoS suna amsar Naira 100 ne idan mutum zai cire tsakanin Naira 1,000 zuwa Naira 5,000, sai kuma Naira 200 idan zai cire fiye da Naira 5,000 ko kuma kasa da Naira 10,000.