Babban Jigo a Jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi ikirarin cewa, masu cewa dan takarar shugaban kasa a NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwakwaso, ya yi wa Peter Obi takarar mataimaki ba ‘yan siyasa bane.
Galadima, ya sanar da hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Arise, inda ya cr gwagwarmayar siysar Kwakwaso ta faro ne tun a shekaru 32 da suka wuce, inda kuma ta Obi, ta faro a cikin watanni biyu kacal.
- Magidanci Ya Kone Gidansa Saboda Matarsa Ta Bata Masa Rai
- ‘Yan Sanda Sun Kama Wata Mata Da Ta Sace Yarinya A Anambra
Ya kara da da cewa babu wani dan siyasa a kasar da ya yi irin aikin da Kwakwaso ya yi a lokacin da ya ke rike da madafun Iko, inda ya kara da cewa Obi ya rike mukanin gwamnan jihar Anambra ne kawai.
Galadima ya kara da cewa, Kwankwaso ne kawai ya fi cancantar zama sabon angon Nijeriya a zaben 2023.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp