Hukumar bunkasa aikin noma ta kasa (NALDA), ta rabawa masu kiwon Kajin gidan gona su 103, ‘yan tsaki 2,500 da abincin Kaji da Kejin yin kiwo a jihar Legas.
Taron rabar da kayan na kwana biyu, na daga cikin shirin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wanda aka rabar da kayan ta hanyar NALDA.
- Wata Iska Mai Karfin Gaske Ta Barnata Gonakin Kaji Da Kashe Sama Da 3,600 A Jihar Filato
- An Gano Ciwon Ciki Da Ke Turnuke Sojojin Isra’ila A Gaza
Shugaban sashen injiniyoyi na hukumar NALDA Injiya Olusegun Owolabi ne ya wakilci babban jami’in hukumar da ke Abuja, Prince Paul Ikonne, a taron rabar da kayan.
Paul ya sanar da cewa, manufar bayan da taimakon ga wadanda suka amfana, shi ne domin a tallafa wa masu kiwon, musamman domin a rage shigo da Kaji daga kasar waje zuwa cikin kasar nan.
Ya ce, wadanda suka amfana da taimakon, an zabo su ne daga yankuna shida na kasar nan.
Paul ya bayar da tabbacin cewa, hukumar za ta ci gaba da gudanar da shirin amma ya danganta yadda masu kiwon da suka amfana suke tafiyar da kiwata Kajin da aka raba masu don kiwata wa.
Ya kara da cewa, duk wanda ya amfana da taimakon mace ko namji, za a kara masa wasu Kajin zuwa guda 48.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana da taimakon Mista Taiwo Ajayi da Grace Oladele, sun godewa gwamnatin tarayya kan samar da shirin.
Sun kuma yi alkawrin yin aiki tukuru, don su samu cin nasara a cikin sana’ar ta su ta kiwon Kajin.