Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Lahadin da ta gabata ya ce matakin da babban bankin Nijeriya (CBN) ya dauka na kaddamar da sabbin kudade da kuma maye gurbinsu da wasu ya samu goyon bayansa kuma yana da yakinin cewa al’umar Nijeriya za su ci riba mai yawa ta yin hakan.
Da yake magana a hirar da wani gidan rediyon Hausa ya yi da fitaccen dan jarida Halilu Ahmed Getso, da Kamaluddeen Sani Shawai da aka gabatar a tashar Tambari TB, Shugaba Buhari ya ce dalilan da CBN suka ba shi sun tabbatar masa da cewa tattalin arzikin kasar zai ci gajiyar yin hakan da kuma samun saukin hauhawar farashin kayan masarufi da magance karakainar jabun kudi da kuma samun karin yawaitar kudaden da ke yawo a cikin Al’uma.
- Yadda BBC Hausa Ya Karrama Gwarazan Gasar Waƙa Da Hikayata Ta Bana
- Sake Fasalin Naira: Emefiele Ya Tabbatar Ba Za A Cire Rubutun Ajami Ba – Sanusi
Ya ce bai dauki tsawon watanni uku na canjin sabbin takardun kudi a matsayin gajeren lokaci ba, saboda idan dai kudin an same su ta hanyar halali hakan ba zai zama damuwa ba.
“Mutanen da ke da kudaden haram da aka binne a karkashin kasa za su fuskanci kalubale da wannan amma ma’aikata da kudaden kasuwanci ba za su fuskanci matsala ba.”
A cikin hirar, shugaban ya kuma yi tsokaci kan batutuwan da suka shafi samar da abinci da tsaron kasa da dai sauransu.
Duk lokacin da gwamnati ta fito wanda yake bako ga al’ummar kasa, ko kuma za ta sauya fasalin wani nata, masana a wannan fannin kan yi wa gwamnatin da al’ummar kasa ammfanin wannan tsari ko kuma rashin amfaninsa ga al’ummar kasa.
A wannan karon batun da ya mamaye kasar nan shi maganar canjin kudi, wanda ya zo da rudani. Daga cikin rudanin da aka samu shi ne, cewa, minister kudi da kasafin kudi da tsare-tsaren kasa Zainab Ahmed, ba ta amince da wannan tsarin na sauya fasalin kudin ba.
Shi kuwa, gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefele, ana cikin wannan dambarwar ya sanar da cewa, za a sake fasalin akardun kudi na naira 200 da naira 500 da kuma naira 1,000.
Sai dai a wannan dambarwar da ake tsakanin minister da gwamnan babban bankin na Nijerya, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana karara cewa, ya ba babban bankin Nijeriya cikakken goyon baya na sake fasalin wasau takardun kudin na Nijeriya.
Wani masani tattalin aezikin kasa kuma tsohon manajan nankin Furst Banka da ke Zariya, mai Suna Sani Mamuda Madobi, ya ce, wadanda suka tattara kudin haram masu dimbin yawa, da kuma wasu daga cikin manyatan ‘yansiyasa da suka taskace kudi a wara maboya, ba za su so wannan scanjin kudi ba, saboda kusan kashi 70 daga cikin kasha 100 na kudin nasu, sun boye su ne Za dai a sauya fasalin naira 200 da naira 500 da kuma naira 1000.
Kamar yadda wasu mutane da dama ke hangen wannan canjin kudi, suna ganin ya zo a daidai lokacin da ya kamata domin ana has ashen cewa, wasu manyan ‘yansiyasa sun taskace kudi, suna jiran a fada kamfen gadan-gadan su yi amfani da su wajen saye ‘yancin jama’a,
Su ma a nasu hangen wasu jam’iyyun na ganin wannan matakin da gwamnati ta dauka, kamar yadda wasu jam’iyyun suka bayyana, babu wanda zai ki wannan shiri na babban bankin na sauya kudi sai dai ‘yansiyasar da ke amfani da makudan kudi wajen saye ‘yancin jama’a.
Sai dai akwai ra’ayi mabambanta daga ‘yan Nijeriya dangane da wanna canjin kudi da za yi. Wadansu na ganin yin hakan zai taimaka wajen saukaka wahalhalun da al’ummar kasar nan ke ciki, domin kuwa dole za ta sa a fito da kudaden da aka boye. Domin da zarar ba a fito da su ba aka canja zuwa sabbin kudin ba har aka rufe canjin sun zama marasa amfani.
Sai dai abu da wani dankasuwa ya lura shi ne, yadda wasu da suka taskace kudin suka fito da su, suna yin ciko kayan amfanin gona da kuma wasu kadarori, wanda hakan ta sa kayan amfanin gonar suka fara tsada tun a wannan lokaci, da ya kamata a ce, suna sauki, yadda talaka zai iya sayen kayan abinci ba tare da fargaba ba.
Saboda haka wasu masu nazari a kan halin rayuwar dan’adam na ganin, duk da wahalar da za a fuskanta a wannan hali, za a warware nan gaba kadan. Kamar yadda suka ce, wannan hanyar na daga cikin hanyoyin da a bi wajen farfado da tattalin arzikin kasar da na al’umma.
Wasu na danganta wahalhalun da ake fuskanta a halin yanzu a wannan kasa da talaucin da ake ciki, da rashin zagayawar kudaden a hannun al’ummar kasa.
Don haka ake ganin wannan mataki da gwamnati da dauka na canjin kudi, zai sa a rage facaka da kudade musamman ga ‘yansiyasa wajen saye ra’ayin mutane.
Kowane abu na da amfani da kuma rashin amfani, sai dai abin da aka fi so shi ne amfanin ya rinjaya, kamar yadda wannan canjin kudin yake, idan aka duba za a ga cewa, amfanin da ke cikinsa ya fi rashin amfanin yawa kamar yadda wasu nasanan suka bayyana.