Makarantu masu zaman kansu da ke Abuja na fuskantar wani gagarumin karin kudin makaranta sakamakon wani gagarumin matakin da Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike ya dauka na kara kudaden gudanarwa da ayyuka a makarantu masu zaman kansu a cikin birnin tarayya.
A karkashin wannan sabon tsarin harajin, kowace makaranta za ta biya kudin kowani dalibi daga cikin adadin daliban da suke karatu a makarantar.
- Shettima Ya Kaddamar Da Kwamitin Mutum 37 Kan Sabon Tsarin Mafi Karancin Albashi
- Karuwar Rincabewar Tsaro: Manyan Hafsoshi Sun Shiga Tsaka Mai Wuya
A wata sanarwa daga babban jami’in kula da asusun sashin tabbatar da ingancin ilimi na sakatare, Mudi Muhammed, wanda wakilinmu ya ci karo da ita a ranar Litinin, na cewa, matakin zai fara aiki ne daga watan Janairun 2024.
A sanarwar mai taken ‘Bita kan kudaden gudanar da ayyuka a makarantu masu zaman kansu a babban birnin tarayya’ na zuwa ne bayan amincewa da ministan babban birnin tarayya ya yi kan sake waiwayar kudaden gudanarwar makarantu da suka kunshi kudaden makaranta na shekara-shekara, wuraren kwanan dalibai, cike bukata, sake sahalewa, farawa aiwatarwa da amincewa, da makarantu masu zaman kansu ke biya.
Wasikar na cewa, “Dangane da wannan wasikar ana sanar da ku cewa daga ranar 31 ga watan Disambard 2023, an canza tsoron farashin kuma sabon tsarin kudin makarantu zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairun 2024.
“Kan sabon tsaron, kowace makaranta za ta biya kudin kowani dalibi adadin daliban da suke makarantar. Daga yanzu kowani Afilikeshin zai koma naira 40,000.”
Kan wannan, shugaban kungiyar makarantu masu zaman kansu a Abuja, a wata wasikar da ya aike ga sakataren ilimi, ya lura kan cewa sabon tsaron na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnain tarayya ke alkawarin rage haraji mai yawa, sai kuma aka bage da kara yawan kudaden gudanar da ayyukan makarantu.
A cewarsa, hakan zai shafi iyaye kuma kai tsaye zai iya janyo ficewar dalibai daga makarantu.
Masu makarantun dai sun yi watsi da karin kudin tare da kiran da a gaggauta sake duba lamarin domin daukan matakan da suka dace.