Gamayyar kungiyoyin masan arewa a kudu ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a arewacin Nijeriya da su gaggauta kashe gobarar da ke shirin babbake yankin.
Gamayyar ta bukaci masu ruwa da tsakin su yi kokarin kawar da duk wata bita da kullin da ake yi wa ‘yan arewa, wanda ya samo asali tun daga shekarar 1999 lokacin da aka dawo mulkin dimokuradiyya a kasar nan.
Sin: Rahoto Kan Xinjiang Shiri Ne Da Amurka Da Kasashen Yamma Suka Kitsa
Shugaban gamayyar kungiyoyin masan, Alhaji Ibrahim Ya’u Galadanci shi ya yi wannan kira a madadin daukacin ‘ya’yan kungiyar, wanda ya koka kan yadda ake shafa wa ‘yan arewa kashin kaji tun ana yi a boye har an fara yi a fili.
A cewar gamayyar, akwai sa hannun bata-gari da ke ikirarin su ne shugabannin arewa acikin tsangwamar da ake yi wa yankin arewacin Nijeriya.
“Muna kira da daukacin matasan arewa da su yi gaggawar sauya tunani a kan halin da suka tsinci kansu, domin ana sake kulla wa arewa munakisa, wanda rashin shugabanin masu tsoron Allah ya sa arewacin Nijeriya ta kasa samun ci gaba a fannoni da dama.
“Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wanda dan asalin yankinmu ne na arewa an ci amanarsa, domin wadanda ya ja a jikinsa wajen taimaka masa su ne suke bata masa suna, kuma mun tabbatar da cewa Allah ba zai bar su ba.
“Ya kamata gwamnatin tarayya ta yi gaggawar sauke gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele tare da yin bincike a kansa da sauran wadanda gwamnati take zargi wajen kulla makircin cutar al’ummar Nijeriya.”
Shugaban gamayyar ya ce wannan shi ne sakon kungiyar da take son isar wa da daukacin masu ruwa da tsaki da ke yankin arewacin Nijeriya tare da matasan yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp