Masu Ruwa da tsaki a fannin Man Fetur da Iskar Gas, sun jaddada bukatar kara samar da yin gasa a bangaren Man Fetur da kuma Iskar Gas da ake hakowa a Teku, mussaman domin a kara janyo masu zuba hannun jari a fannin.
Sun yi wannan kiran ne a taron tattaunawa, da kungiyarsu da ake kira a turance ta Edtractibe360 ta hadawa manema labarai a Babban Birnin Tarayyar Abuja.
- Sin Ta Maida Martani Ga Yiwuwar Daukar Matakin Sojan Amurka A Kan Venezuela
- Amfani Da Wutar Lantarki A Sin Ya Habaka Sosai A Watan Yuli
Sun zayyano mahimmancin da ke na yin gasa a fannin, mussaman domin a tabbatar da an tsaftacen bangaren da kuma samar masa, da rasuwar da ta dace.
Daya daga cikin masu ruwa da tsaki a fannin Ademola Adigun, ya jaddada cewa, fannin na hako Man daga Taku, ba wai ana nufin a dakatar da shigo Man daga kasar waje bane duk da ci gaban da aka samu na kafa Matatar Mai ta Dangote a kasar nan.
Ademola ya kara da cewa, kafa Matatar Man ta Dangote, wata babbar nasarar ce ga kasar nan wajen zuba hannun jari wacce kuma ta zamo abin tunkaho ga kasar, amma tana fuskantar rashin samun gasa ta kasuwa na karfin iya tace yawan Man da ake bukata a kasar.
“Dole ne fannin na hako Man daga Taku, ya zamo an samar da gudanar da gasa kuma dole a tabbatar da an yi adalci da bin ka’ida domin masu amfani da Man, su amfana,” A cewar Adigun.
“Samun Matatar Man ta Dangote, wata babbar nasara ce, ta zuba hannun jari a fannin Mai na kasar nan,.” A cewarsa.
“A shekaru baya, Nijeriya ta fi yin dogaro wajen shigo da Man Fetur zuwa cikin kasar, amma bisa samun kafa Matatar Man ta Dangote, labarin ya sauya, kan shigo da Man da sauran dangoginsa zuwa cikin kasar nan daga wasu kasashen waje,” Inji Adigun.
Ya kara da cewa, amma duk da zuba hannun jari a fannin na hako Man daga Taku, har yanzu Fannin na ci gaba da fuskantar karancin samun gasa wajen sarrafa Man da kuma na dangoginsa.
“Nijeriya za ta ci gaba da shigo da Man daga kasar waje amma ba wai domin kasar ta rasa samun kasuwanni bane sai dai kawai saboda rashin samun wani zabin da ya kamata” A cewarsa.
Shi ma a na sa jawabin a wajen ttaron kwararren a bangaren shari’a Olasubomi Chuku, ya zayyano wasu daga cikin matakan na gasar wanda ya danganta a matasyin babbar gasa dake tattare da fannin.
Shugabar ta kungiyar Juliet Ukanwosu ta sanar da cewa, tun lokacin da Gwamnatin Tarayya ta cire tallafin Man Fetur hakan ya sanya an samu daidaito farashin Man Fetur a gidajen sayar da Man da ke a kasar.
A cewarta, hakan ya kara haifar da zazzafar gasa a tsakanin masu hada-hadar kasuwanci na Man a kasar.
“Wannan ya kara sanyawa an samu sauye- sauye a farashin na Man Fetur da haifar wa kasuwanci wani sabon juyi wanda hakan ya kuma shafi masu amfani da Man a yau da kullum, ” Inji Juliet.
Kazalika, Shugabar ta lissafo wasu daga cikin kalubalen da suka hada da, tsadar kudaden aiki da yawan samun hauhawan farashin kudaden musaya na ketare da dogaro kan Man Fetur da ake shigowa da shi cikin kasar nan da kalubalen shigo da kayan aikin da sauransu. wanda hakan ke kara jefa fannin s cikin wani kalubalen.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp