Kungiyar masu sarrafa mai daga waken soya zuwa man girke-girke ta kasa (OSPAN), ta bayyana jarinta na dala miliyan 250 da ta zuba; don sarrafa mai daga Irin Waken Soya, a matsayin wanda ke fuskantar barazana, sakamakon yadda ake fitar da Waken Soyar zuwa kasashen waje.
Wannan korafin na kunshe ne a cikin sanarwar da Shugaban Kungiyar na Kasa, Sama’ila Barau Maigoro da Mataimakinsa, Mista Hule Idyerkas suka sanya wa hannu tare da fitar da shi a Garin Lafiya da ke a Jihar Nasarawa.
- Hizba Ta Gana Da Kungiyar Masu Bege, Ta Bukaci Su Tsabtace Harshe
- Na Fi Jin Dadin Rubutu Da Sassafe Ko Dare – Princess Mazadu
Sanarwar ta yi kira da a haramta fitar da Waken Soya daga Nijeriya zuwa sauran kasashen ketare, domin a karfafa wadanda suke sarrafa Irin Waken Soyar zuwa man girki; kwarin guiwa.
A cewar sanarwar, idan aka sarrafa man daga Irin na Waken Soya zuwa man girki, hakan zai bayar da dama wajen sarrafa ainahin danyen man Waken Soyar da za a rika yin amfani da shi a cikin kasar nan, wanda hakan zai taimaka wajen karya farashin sauran man girki a Nijeriya.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, akwai ‘ya’yan kungiyar manya da matsakaita da suka zuba jarinsu, domin sarrafa mai daga Irin Waken Soya zuwa man girki.
Ta kara da cewa, a yanzu haka man girkin da ake sarrafawa daga Irin Waken Soya a kowace shekara; ya kai tan miliyan uku, inda kuma jarin da aka zuba a fannin ya kai na kimanin dala miliyan 250.
A cewar sanarwar, a yanzu haka mune a kan gaba wajen samar da aikin yi a bangaren aikin noma na fadin kasar nan, domin muna samar da ayyuka na kai tsaye sama da 200,000.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, muna so Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dakta Doris Uzoka-Anite su sani cewa, akasarin masana’antun da ke sarrafa mai daga Irin Waken Soya zuwa man girke-girke a kasar nan, na ci gaba da kullewa sakamakon karancin kayan aiki, musamman Waken Soya.
Bugu da kari sanarwar ta bayyana cewa, Manoman Waken Soya a shekarar 2022; sun noma Waken Soya kimanin tan 680,000, amma maimakon su sayar da shi ga masu sarrafa shi a nan cikin gida, sai suka gwammace fitar da shi zuwa kasashen ketare; domin samun kazamar riba.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, wannan lamarin na ci gaba da zama babbar barazana ga tattalin arzikin wannan kasa tare da jawo koma baya ga kokarin da gwamnatin kasar ke yi na fadada tattalin arziki da kuma kokarin samo wadanda za su zuba hannin jari a fannin tattalin arzikin tare da samar da ayyukan yi a fannin sarrafa Irin Waken Soya zuwa man girki.
Kungiyar ta sanar da cewa, Nijeriya ba ta cikin jerin kasashen duniyar da ke a kan gaba, wajen noman Waken Soya, inda wannan sabon halin na fitar da Waken Soya zuwa ketare ke jawo wa masu sarrafa mai daga Irin Waken Soya a kasar nan babban koma baya.
Kazalika, kungiyar ta OPSAN ta bukaci Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ta kawo musu daukin gaggawa a kan matsalar fitar da wannan Wake na Soya da ake yi zuwa kasashen waje.
Sannan, kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta haramta fitar da Waken Soyar na wucin gadi daga nan Nijeriya zuwa sauran kasashen waje, har sai an tabbatar an samar da wadatuwarsa a fadin wannan kasa baki-daya.
Har ila yau, kungiyar ta kara da cewa, idan aka haramta fitar da Waken Soyar daga wannan kasa zuwa kasashen ketaren na wucin gadi, hakan zai taimaka wajen kara fadadawa da kuma bunkasa masana’antun da ke sarrafa Irin Waken Soyar zuwa na man girki a kasar nan tare da kara bunkasa tattalin arziki da kara samar da ayyukan yi ga ‘yan kasa baki-daya.