Ko kadan babu hannun manoma kan hauhawar farashin kayan abinci da ‘yan Nijeriya ke ci gaba da kokawa a kansa, wasu ‘yan kasuwa masu sayen amfanin gonar ne daga wurin manoma suke saya suna boyewa don sayarwa su samu kazamar riba, don haka su ya kamata mutane su zarga.
Wannan furucin ya fito ne daga bakin fitaccen manomin Masara a Arewacin wannan kasa, Adamu Muhammad Makarfi a wata tattaunawa da ya yi da LEADERSHIP Hausa a Jihar Kaduna.
- NCRMIDP Ta Raba Wa ‘Yan Gudun Hijira 700 Kayan Abinci A Katsina
- Kabilanci Da Magudin Zabe Ke Kassara Samun Shugabanci Nagari – Jonathan
Makarfi, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar manoman Masara don samun riba na Arewa maso yamma ya yi nuni da cewa, duk wadanda ke cewa manoman kasar nan ne suka haddasa hauhawar farashin kayan abinci, ba su yi musu adalci ba.
Shugaban ya ci gaba da cewa, duk da cewa manomi na da burin ganin ya samu riba bayan ya yi girbi, amma kuma ba shi da burin ganin ya tsauwala wa jama’a; musaman talakawa.
Har ila yau, Makarfin ya danganta hauhawar farashin da ake ci gaba da samu na kayan abincin a kan wasu ‘yan kasuwa da ke sayen amfanin gonar manoma, musamman kanana suna boyewa; domin sayar wa da jama’a kan farashin mai yawan gaske.
Hak zalika, ya bai wa gwamnatin tarayya shawara kan tabbatar da samar da tsarin kayyade farashin kayan abinci a fadin wannan kasa baki-daya, a cewar tasa ta haka ne kawai za a iya magance yadda ake ci gaba da samun tashin farashin kayan na abinci a daukacin fadin kasar nan.
Kazalika, shugaban ya kuma bayyana cewa; ya kamata gwamnatin tarayya ta fito da wani tsari na musamman domin dakile wasu ‘yan kasuwa masu zuwa wurin manoma, musamman kanana suna saye amfanin gonarsu cikin rahusa, domin boyewa su sayarwa da al’umma da tsada.
Har wa yau, da yake yin bayani a kan shirye-shiryen noman bana, Makarfiya bayyana cewa; akasarin manoma a kasar nan, musamman kanana ba za su iya yin noma a bana ba.
Ya kara da cewa, bayanai sun nuna cewa; musaman matsalar tsadar takin zamani a bana kusan ya fi na bara, sannan kusan a bana farashin buhun taki duk guda daya a wurin ‘yan kasuwa ya kai kimanin Naira dubu 40 zuwa sama, ya danganta da irin nau’in takin.
A cewar tasa, a kakar noman bara kusan an sayar da takin ne a kan Naira 30,000.
Bugu da kari, shugaban ya sanar da cewa; wata matsalar ita ce ta tsadar magungunan feshin kwari ko na kashe ciyawa da kuma kalubalen biyan kudin ‘yan kwadago da sauransu.
Ya ci gaba da cewa, a matsayinsu na manoma bukatarsu ba wai kawai a sayar da amfanin gona da tsada a wannan kasa ba ne, amma duk da haka, ba za su so a ce manoma sun yi asara ba, domin asarar manoma; asara ce ga kasa baki-daya.
Sannan ya yi nuni da cewa, duk inda aka ce manomi ya yi noma kuma ya fadi, babban abin da ake jin tsaro, musamman ma ga manyan manoma wadanda yawancin su suke yin noman, domin su samu riba; da zarar an ce sun fadi an samu matsala; don kuwa akasarinsu suna ciwo bashi ne daga bankuna, domin yin noma da kuma kudin ruwan da ake dora musu, saboda haka asarar za ta yi musu yawa.
Adamu ya ci gaba da cewa, idan manyan manoma ba su yi noma a kasar nan ba, ko shakka babu za a samu karancin abinci, wannan dalili ne ya sa ake yin kiraye-kiraye, don zuwa kasashen ketare a sayo abincin, sannan idan aka sayo abincin daga ketare, Nijeriya za ta iya yin asara mai yawan gaske, domin hakan zai iya durkusar da tattalin arzikinta.
Haka zalika, ya yi nuni da cewa, idan misali aka je aka sayo tan miliyan biyu na Masara don shigo da shi Nijeriya, sai an kashe akalla kusan Naira tiriliyan daya, sannan ban da sauran amfanin gona; kasar nan na bukatar akalla tan miliyan ashirin.
Ya ce, in har za a sayo Masara a kasar waje ba a noma cikin gida ba, akalla za mu yi asarar zunzurutun kudi kimanin Naira tirilyan goma, saboda haka; idan ba a bai wa manoman wannan kasa taimakon da ya dace ba, ba karamar matsala ce za ta afku ba.
Sannan, ya yi kira na musamman ga gwamnatin tarayya da ta jihohi da kuma kananan hukumomi, su mayar da hankali wajen bunkasa noman rani, domin kuwa a cewar tasa ya zama wajibi a samar da kyakkyawan tsari, amma idan ba a yi hakan ba; ba mu san irin abin da zai faru a wannan kasa ba.