A yau, Adabi ya yi tozali da daya daga cikin marubuta da ke ba da gudunmawarta ga al’umma ta fannin rubutu wato MARYAM BALA MIKA’IL wacce aka fi sani da SAKATARIYA a duniyar marubuta. Marubuciyar, ta haska wa masu yunkurin fara rubutu wasu hanyoyi da ya kamata su bi kafin su fara rubutun, ta kuma ba wa sauran marubuta shawara game da abin da ya kamata su rika yi da zarar sun zama sannanu, har ma da wasu baututuwan masu yawa. Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu RABI’AT SBS (BIG GAL) Kamar haka:
Ya sunan marubuciyar?
Sunana Maryam Bala Mika’il, wacce aka fi sani da Sakatariya.
Ko za ki fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
Masha Allah! Da farko dai sunana Maryam kamar yadda na fada a baya. Ni haifaffiyar garin zuru ce dake Jihar Kebbi, ina zaune a garin Ibadan ina da aure wanda Allah ya albarkance ni da ‘Ya, Alhamdulillah.
Me ya ja hankalink har ki ka tsunduma rubuce-rubuce?
Abin da ya ja hankali na shi ne; Kawaye, yadda na ga suna rubutu sai ni ma ina sha’awar abun, musamman wajen mika sakonnin da mutum ya ke son isarwa ga al’umma.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
To sai dai mu ce Alhamdulillah, tunda mun samu masu goya mana baya, kuma ba tare da mun sha wahala ba, har hakan ya kasance.
Daga lokacin da ki ka fara zuwa yanzu, kin rubuta labarai sun kai kamar guda na-wa?
To, Alhamdulillah na rubuta labarai a kalla za su kai goma.
Kamar wane irin labari ki ka fi maida hankali a kai wajen rubutawa?
Na fi maida hankali a kan labarin da ke faruwa na yau da kullum.
Wane labari ne ya zama bakandamiyarki cikin labaran da ki ka rubuta?
Wanda ya zama bakandamiyata shi ne; Fyade 2020, na yi shi ne a kan Fyade wanda a lokacin abun ya yawaita sosai.
Wane labari ne ya fi baki wuya wajen rubutawa?
Komai Nisan jifa, saboda labari ne da ya shafi matsalolon kishiyoyi, kuma ina yi ina buncike.
Ya batun maigida lokacin da ki ka fara sanar masa za ki fara rubutu, shin kin samu wani kalubale daga gare shi ko kuwa?
A’a, babu wani kalubalai dana fuskanta.
A labaran da ki ka rubuta ko akwai wanda ki ka buga?
A’a! Gaskiya babu wanda na buga sai dai ina saka ran bugawa.
Wane irin nasarori ki ka samu game da rubutu?
Akwai nasarori da dama wanda sai dai mu ce Alhamdulillah, dan baki ma ba zai iya fadarsu ba.
Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta game da rubutu?
Gaskiya akwai su, sai dai kin san wani kalubalan matakin nasara ne.
Mene ne burinki na gaba game da rubutu?
Gaskiya a yanzu ba ni da wani buri ko ra’ayin rubutu sai dai nan gaba.
Ko an taba bata miki rai Ko faranta miki sanadiyyar rubutu?
Eh! tabbas an taba yi mun dukka biyun.
Wane abu ne idan ki ka tuna shi ki ke jin dadi sanadiyyar rubutu?
Idan na tuna yadda rubutu ya hada ni da mutane da dama.
Ya kika dauki rubutu a wajenki?
Hanyar Fadakarwa.
Kamar da wane lokaci ki ka fi jin dadin yin rubutu?
Na fi jin dadin yin rubutu da dare.
Me za ki ce da masu karanta labaranki?
Ina yi musu fatan alkhairi kar su manta su ne ni, ni ce su.
Me za ki ce ga masu kokarin fara rubutu?
Abin da zan ce musu shi ne; na farko su zamo masu karatu a kodayaushe, na biyu su yi hakuri ga dukkanin artabon da za su tsinci kansu, sannan ban da satar fusaha, su kwafi na wani su canja suna ko su kalli fim su mayar da shi labarin littafinsu da sunan nasu ne, su saukar da kansu ga masu koya musu rubutu duk da cewa shi rubutu bai-wa ce wadda ba koya a ke yi ba sai dai ka koyi yadda za ka tsara shi da kuma yadda za ka tafiyar dan masu karatu su karanta, kar su zama masu yin butulci ga wadanda suka dora su a kan hanya, ko da kuwa za su ci karo da wasu, wannan a takaice kenan.
Ko kina da wata shawara da za ki ba wa sauran marubuta?
Shawarata ga marubuta; su zamo masu saukin kai, su cire girman kai a duk lokacin da suka tsinci kansu a wata hanya ta ci gaba, sannan su taimaka wa na kasa masu tasowa kar su wulakanta su dan gudin kamar za su zo su fi su idan sun karbe su, su zamo masu hadin kai, ban da cin naman wani ko aibata wani matsayinsu na marubuta, duk abin da za a ji wane ya ce ko wane ya yi, a kawar da shi muddin ba daga bakinsa a ka ji ba. Allah ya sa mu dace.
Me za ki ce da masu karanta hirar nan ta ki?
Ina yi musu fatan alkhairi, ina godiya kuma su ci gaba da bibiyar wannan shafi na Adabi domin jin ta bakin marubuta.
Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Eh! Tabbas, da fari ina gaida Rabi’at ‘Yar Sidi (Big GaL), sannan ina gaida Shamsiya l. Rabo, ina gaida Fateema Lawal Zahraty, ina gaida Fateema Zee-Zee, ina gaida Rukayya Ibrahim Waheeda, sannan ina gaida Fateema Ibrahim.
Muna godiya sosai, ki huta lafiya.
Ni ma na gode, Allah ya kara daukaka gidan jaridar LEADERSHIP musamman LEAD-ERSHIP Hausa.