Wasu mata biyu sun gamu da ajalinsu yayin da wasu uku ke kwance suna karbar magani sakamakon raunukan da suka samu a ruftawar ramin da ya rutsa a wajen hakar ma’adinai a Bar Kudu da ke karamar hukumar Bogoro a Jihar Bauchi.
Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Bogoro a Majalisar Dokokin jihar Bauchi, Hon. Musa Wakili Nakwada, shi ne ya sanar da hakan a gaban kwaryar Majalisar sa’ilin zamanta na ranar Alhamis wanda mataimakin Kakakin Majalisar Danlami Ahmed Kawule ya jagoranta.
- Gwamnan Gombe Ya Nada Mai Rikon Safiyo-Janar Da Babban Jami’in Kididdiga
- Yanzu-yanzu: Sojoji Sun Yi Watsi Da Kaloli 53, Sun Fitar Da Sabbi 28 A Abuja
A cewarsa ibtila’in ya ritsa da mata biyar ne, “Biyu sun mutu, sauran ukun kuma da suka tsira da raunuka daban-daban suna amsar kulawar Likitoci.”
Ya ce, an kammala shirye-shirye bisne mamatan biyu.
Hon. Nakwada ya bukaci Majalisar da ta aike da sakon ta’aziyya da jajantawa tare da addu’ar neman sauki ga wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata.
Da ya ke maida jawabi, Kakakin Majalisar Dokokin jihar, ya aike da sakon ta’aziyya da jajantawa ga al’ummar mazabar Bogoro tare da kira ga shugaban karamar hukumar da ya tabbatar an taimaka ma wadanda lamarin ya shafa.