Asma’u Kabir, matashiya ce kuma ‘yar kasuwa wadda tun tana karamar makarantar sikandire wato JSS 1 ta fara. Ta bayyana yadda ta fara sana’a da irin nasarar da ta samu da kuma kalubale kai har ma da shawarwarin da ta ba wa mata don su tashi tsaye su nemi na kansu domin zama haka ba dace da mata a yanzu ba. Ga dai yadda hirar ta kasance:
Da fari za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki
Da farko dai suna na Asmau Kabir Machika, na yi firamare a Ideal International School Funtua, na yi JSS 1 zuwa 3 ma can, sai na je GGSS Kaikai na karasa S S 1 zuwa 3.
Shin kina da aure?
Eh ina da aure da ma da daya.
‘Yar kasuwa ce ko kuma ma’aikaciya ce?
Eh ni a gaskiya na hada duka kasuwancin da aikin, kowanne ina yi sai dai fatan Allah ya sa mana albarka.
Wanne irin kasuwanci kike yi?
Kasuwancin da nake yi na intanet ne, a nan nake sai da kayana gaskiya.
Shin me kasuwancin naki ya kunsa, Ma’ana kamar me da me kike sarrafawa?
Ina kawo kayan yara da kayan kicin, kuma ina sayar da kamar su turaren wuta, oil perfumes, sannan ina yin local candies (kamar su tsami gaye, Gullisuwa, mandula da dai sauransu).
Me ya ja hankalinki har kika shiga wannan kasuwancin?
Ai ni kasuwanci da shi na tashi gaskiya tin ina JSS 1 2 na fara daga kan ‘yan gidanmu ina sayar masu su kadai da dai na ga eh ana samun riba kawai sai na dore, na fara tallatawa ‘yan waje kuma na samu kasuwa sosai shike nan daga nan na tsunduma da saye da sayarwa.
Mene ne matakin karatunki?
Matakin karatuna shi ne digiri, daga nan na tsaya
Wanne irin kalubale kika taba fuskanta a cikin sana’arki?
Kalubalen da nake fuskanta shi ne bashi a sayi abu kana ji kana gani a hana ka kudi, wani ma idan ka tambaya sai a ga ka yi gajen hakuri wata ma ta gaya maka maganar da za ta bata maka rai, sannan kuma mutane wasu da yawa ba sa gane yadda rayuwar ta koma, sai ki ga suna hada kudin da da na yanzu alhalin kuma ba haka ba ne, yanzu komai ya canza, sai su rinka ganin kamar mutane suna tsadar kaya ne ai komai ya yi tsada yanzu.
Zuwa yanzu wadanne irin nasarori kika samu?
Nasarorin da na samu Alhamdulillah, an samu ci gaba sosai sai dai kawai addu’ar Allah ya kara rufa mana asiri.
Wanne abu ne ya fi faranta miki rai game da sana’arki?
Abin da ke faranta min rai game da sana’ata shi ne idan aka sayi daya daga cikin abin da nake sayarwa mutum ya ce ya yi masa to wannan yana faranta min rai sosai.
Wacce hanya kike bi wajen tallata kayan sana’arki?
Hanyar da nake bi wajen tallata sana’ata sune Whatsapp, Instagram, Tik-tok.
Dame kike so mutane su rinka tunawa da ke?
Ina son mutane su rinka tinawa da ni ta abubuwan da nake sayarwa masu nagarta da yadda suke jin dadin mu’amala da ni ta hanyar kasuwancina.
Ga hidimar gida, ga kuma hidimomin sana’a, shin ta yaya kike samun damar gudanar da hutunki?
Hanyar da nake samun gudanar da sana’ata gaskiya ta zo min da sauki, saboda sana’ata ta intanet ce don haka da waya nake komai, saboda haka gaskiya ina samun hutu sosai ba ni da matsala.
Wace irin addu’a ce idan aka yi miki kike jin dadi?
Gaskiya ina jin dadin wannan addu’ar idan aka yi min ita, Allah ya jikan iyaye, da kuma addu’ar Allah ya karo kasuwa mai albarka.
Wanne irin goyon baya kike samu daga wajen iyaye da ‘yan uwanki?
Gaskiya ina samun goyon baya sosai daga wajen iyaye na da kuma ‘yan uwana suna taya ni da addu’a sannan kuma suna karfafa min gwiwa musammam ma ‘yan uwana da suke taya ni sa hotonan kayan sana’ata.
Kawaye fa?
Kawaye ma Alhamdu lillah suna ba ni goyon baya yadda ya dace suma suna sa hotunan kayan sosai.
Me kika fi so cikin kayan sawa da kayan kwalliya?
Cikin kayan sawa ina son Atamfa.
A karshe wanne irin shawara za ki ba ‘yan uwanki mata?
Shawarar da zan ba ‘yan uwana mata shi ne su tashi su nemi sana’a su samu abin yi zaman haka ba dadi, kuma a yi ta addu’ar Allah ya sa albarka.