Hassana Umar Sani Matashiyar daliba a bangaran sanin cututtuka a makarantar Babura da ke Jihar Jigawa, ta shawarci mata da su dage da neman ilimi da kuma neman na kansu. Hassana ta bayyana haka cikin tattaunawarsu da wakiliyarmu BILKISU TIJJANI ALKASSIM, inda ta kara da bayyana mata irin nasarorin da ta samu da kuma kalubalen da take fuskanta a rayuwar makaranta, kamar dai yadda za ku karanta. A sha karatu lafiya.
a fari za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki?
Suna na Hassana Umar Sani, ni haifaffiyar garin Kano ce, na yi firamare a Al’amin Nursery and Primary School, na yi sakandire dina a Key Science GSTC Kano.
Shin Hassana matar aure ce?
A’a ba ni da aure
Malama Hassana kina da wata sana’a ne ko kuma karatun aka sa a gaba?
Eh to a gaskiya yanzu ba ni da wata sana’a, karatu na sa a gaba, ni daliba ce a makartar lafiya dake Karamar Hukumar Babura.
Me kike karanta?
A bangaran sanin cututtuka ne
Me ya ja hankalinki da har kike sha’awar wannan karatun?
Saboda ina son sanin cututtuka da maganinsu, sannan na san idan wata cuta ta kama dan’Adam na san yadda zan bollo wa maganinta, ko wacce irin cuta na san yadda za a magance ta.
Hassana baki fada mana matakin karatunki ba?
National Diploma a shekarar karshe
Wanne irin kalubale kika taba fuskanta a cikin karatunki?
Na taba fuskantar kalubale wajen wani malami da nake da tabbacin na ci jarabawarsa kuma ya kayar da ni, saboda can wani abinsa da kuma san ransa shi ya sa ya kayar da ni.
Zuwa yanzu wadanne irin nasarori kika samu?
Nasarar da na samu shi ne na koyi abin da nima zan taimaka wa wasu mutane da dama, suma su ci moriyar abin. Ina ganin wannan ba karamar nasara bace a wajena.
Wanne abu ne ya fi faranta miki rai game da karatunki?
Abin da yake farantamin rai game da karatu na shi ne ina son in ga na koyi abu kuma na iya shi sosai, wannan gaskiya ba karamin faranta min rai yake ba.
Da me kike so mutane su rika tunawa da ke?
Ina so mutane su rika tunawa da ni akan abin alkhairi na da kuma kokarina da jajircewata
Kasancewar ke dalibar lafiya ce ance akwai tsananin katatu, ta yaya kike samun gudanar da hutunki?
Ina samu na yi karatu ta hanyar rashin yawan mutane a waje, to ya fi min sauki, wato idan waje ya yi shiru to gaskiya ina saurin fahimtar karatu cikin kankanin lokaci, har na samu na dan huta.
Wace irin addu’a ce idan aka yi miki kike jin dadi?
Addu’ar ci gaba a rayuwa ta duniya da lahira, idan aka yi min wannan addu’ar gaskiya ba karamin jin dadinta nake ba.
Wanne irin goyon baya kike samu daga wajen iyaye da ‘yan uwanki?
Ina samun goyan baya daga wajen iyayena sosai ta hanyar kwarin gwiwa da kulawarsu da suke bani, na gode musu sosai.
Kawaye fa?
Eh suma suna bani shawarwari ta hanyar karatu
Me kika fi so cikin kayan sawa da kayan kwalliya?
Inason dogayen riguna sosai , kayan kwalliya kuma ni ba ma’abociyar kwalliya bace duk abin da na samu ina amfani da shi
A karshe wanne irin shawara za ki ba ‘yan uwanki mata?
Ina so ‘yan uwana mata mu dage da neman ilimi kuma mu dage da neman na kanmu. Allah ya taimake mu baki daya.