FATIMA ABDULLAHI haifaffiyar Hadejia, kuma yar kasuwa mai neman na kanta, ta tattauna da shafin Adon Gari inda ta yi bayanin yadda ta tsinci kanta a matsayin ‘yar kasuwa mai zaman kanta, nasarorin da ta samu ta da kuma irin kalubalen da ta fuskanta wajen kafa sana’arta da kuma yadda take sarrafa ta, inda a ciki ta shawarci mata kan lallai su tsare mutuncinsu a duk inda suke, domin idan sun yi haka Allah zai kawo musu mafita, ga dai yadda tattaunawar tasu ta kasance tare da BILKISU TIJJANI KASSIM:
Da fari za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki
Fatima Abdullahi Muhammad. Iyaye na haifaffun Jihar jigawa ne cikin Karamar Hukumar Hadejia. Na girma a Garin Kano na yi makaranta a Kano kuma ni ce ta farko a wajen mamana da babana. Wannan ne takaitaccen tarihina.
Shin ke matar aure ce?
A’a ba ni da aure, muna dai niyya in sha Allahu.
An kusa auran kena?
Eh to kin san da yake aure mukaddari ne daga Ubangiji, sai ki ga wani idan ya zo babu bata lokaci an yi shi duk zaman da ka yi sai ki ga ya wuce an manta da shi. Yanzu dai gaskiya takamaimai babu maganar aure muna sa ran Allah ya kawo mana miji nagari.
Malama ‘yar kasuwa ce ko kuma ma’aikaciya?
Eh ni ‘yar kasuwa ce
Wanne irin kasuwanci kike yi?
Ina saida abubuwa da dama
Me ya ja hankalinki har kika shiga wannan kasuwanci?
Eh to a gaskiya ni tun ina karama ina ganin ana kasuwanci kuma tun lokacin yake matukar burgeni har na girma ina sha’awar kasuwancu kuma yana matukar birge ni, ni dai ina sha’awar na zama mai saye da sayarwa.
Mene ne matakin karatunki?
Matakin karatu na shi ne N.C.E. daga nan na tsaye ban ci gaba ba.
To amma kina sha’awar ciga da karatunki ne ko kuma kasuwancin kikasa a gaba?
Gaskiya ina da ra’ayin ci gaba da karatu kuma in sha Allahu ina sa ran hakan.
Wanne irin kalubale kika taba fuskanta a cikin sana’arki?
A gaskiya kin san ko wace sana’a ba ta rasa kalubale sai dai mu ce Alhamdu lillah. Babban kalubale na shi ne bai wuci maganar bashi ba mutane su dauki kaya ba sa son biyan kudi wani idan kai wa miutum magana ya nemi ya gaya maka maganar banza kai da kayanka aka dauka, wani kuma ma ba zai bayar ba sai ka zo ka yi ta rigima har ka bar shi wasu kuma ba sa son daukar kayan idan ba su da kudi wadanda ke tsoron Allah kenan, wani kuma idan ya dauka daga ya samu zai bayar, to kin gani ba za a taba kasuwanci a ce babu bashi ba sai dai ka san wanda za ka ba wa. Allah ya bamu kasuwa mai albarka.
Zuwa yanzu wadanne irin nasarori kika samu?
Alhamdu lillah mun samu na sarori da dama ana ta samun ci gaba, kasuwanci yana ta bunkasa sosai ma, Allah mun gode maka.
Wanne abu ne ya fi faranta miki rai game da sana’arki?
Ina matukar jin dadi wajen biya ma kaina bukatu ba tare da na tambaya a yi min ba wannan gaskiya yana faranta min rai sosai har ma ina taimaka wa wasu Alhamdu lillah.
Ta wacce hanya kike bi wajen tallata sana’arki?
Kafar sada dumunta, kamar WhatsApp, Face book, insgram, da dai sauransu.
Dame kike so mutane su rika tunawa da ke?
Kyawawan halayya da kuma kokarin cika alkawari na, da kuma idan mutum ya sayi kayana hankalina ba ya kwanciya har sai kayan ya shiga hannunsa ya tabbatar min da abin da ya saya ya samu.
Wanne irin addu’a ne idan aka yi miki kike jin dadu?
A ce min Allah ya jikan mahaifiyata a gaskiya duk wanda ya ce min Allah ya jikan mahaifiyata ba karamin jin dadi nake ba kuma wanda ya fada min yana shiga raina.
Wanne irin goyon baya kike samu daga wajen iyaye da ‘yan uwanki?
Sun bani goyan baya dari bisa dari.
Kawaye fa?
Su ma suna ba ni hadin kai sosai suna kuma taya ni tallata kayana na gode musu.
Me kika fiso cikin kayan sawa da kayan kwalliya?
Cikin kayan sawa na fi son abaya ko atamfa, kayan kwalliya kuma gaskiya ni abociyar kwalliya ce ina son kowanne in dai zan yi amfani da shi ya yi min kyau to gaskiya ina son shi.
A karshe wace irin shawara za ki ba ‘yan uwanki mata?
Su dage da neman na kansu.kum su rike mutuncin su a duk inda suke. Sannan kuma su rike gaskiya da amana a kowane hali mutum ya tsinci kanshi Allah zai kawo mafita.