A farkon wannan makon ne,iyaye mata suka dakatar da hada-hada karamar hukumar Wukari ta jihar Taraba, sakamakon yawan sace musu kananan yara da ake yi.
Aun shirya zanga-zangar ce, domin su nuna damuwarsu kan yawan bacewar kananan yara a wannan yanki nasu.
Masu zanga-zangar sun ce, a cikin wannan lokacin kadai sama kananan yara guda takwas aka sace.
Masu zanga-zanga sun fito suna cewa, a fito musu da yara guda takeas din da aka sace kwanan nan.
Datake jawabi a wajen wannan zanga-zanga, Justin Ajifken ta ce, a kwanan nan yara da dama sun bata a wannan yanki nasu. Ta ce, “yanzu haka rahotannin da suka samu, yara takwas sun bace”.
Saboda haka sai matan suka bukaci hukuma da ta gaggauta daukar dukkan matakan da suka dace domin kawo karshen wannan sata ta kananan yara. Yaran da aka sace, kusan bas a wuce shekara shida.
Da aka nemi jin ta bakin shugaban karamar hukumar, Daniel Adi, ya karyata cewa, an yi zanga-zanga a karamar hukumar, sai dai ya tabbatar da cewa akwai wasu yara da suka bata ake nemansu, kuma har zuwa lokacin hada wannan labara ba a gansu ba.
Ya ce, jami’an tsaron sun gargadi mutane kan yada jita-jita, wanda ya ce hakan na lya haifar da tayar da zaune tsaye.