Mataimakin babban magatakardan MDD, kana sakataren zartarwa na kwamitin tattalin arzikin Afirka Claver Gatete, ya bayyana cewa, kasar Sin aminiya ce da kasashen Afirka za su iya dogaro da ita.
Gatete ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin da ya karbi takardar wakilcin kasa daga sabon wakilin kasar Sin a kwamitin tattalin arzikin Afirka na MDD, kana shugaban tawagar jakadun kasar Sin dake kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU Jiang Feng a birnin Addis Ababan kasar Habasha, mazaunin kwamitin na tattalin arzikin Afirka na MDD.
A yayin ganawarsu, Claver Gatete ya taya Jiang Feng murnar gudanar da sabbin ayyuka, ya kuma yi fatan karfafa hadin gwiwa da kasar Sin, domin ba da taimako ga bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin. Haka kuma, ya yi matukar jinjina ga manufar cire haraji kan hajojin Afirka da kasar Sin ta fidda.
A nasa bangare kuwa, Jiang Feng ya ce, kasar Sin tana fatan hada kai da kwamitin tattalin arzikin Afirka, wajen aiwatar da sakamakon da aka cimma a taron koli na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka na Beijing, tare da gina makomar al’ummun Sin da Afirka ta bai daya. (Mai Fassara: Maryam Yang)














