Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng da sakatariyar baitulmalin kasar Amurka Janet Yellen sun yi tattaunawa da dama a birnin Guangzhou da ke kudancin kasar Sin, daga ranar 5 zuwa 6 ga watan Afrilu, inda bangarorin biyu suka mai da hankali kan aiwatar da muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, sun kuma yi musayar ra’ayi mai zurfi cikin gaskiya kuma mai ma’ana kan yanayin tattalin arzikin kasashen biyu da na duniya, da dangantakar tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka, da kalubalen da duniya ke fuskanta.
Bangarorin 2 sun amince su tattauna batutuwan da suka hada da daidaiton ci gaban tattalin arzikin Sin da Amurka da na duniya, da daidaita harkokin kudi, da dorewar harkokin kudi, da hadin gwiwa wajen yaki da halatta kudin haram, a karkashin tawagar aiki ta kasashen Sin da Amurka mai kula da harkokin tattalin arziki da hada-hadar kudi. Haka bangaren kasar Sin ya nuna matukar damuwa kan takaitawar da Amurka take sanyawa kasar Sin ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, tare da mayar da martani sosai kan batun karfin samar da hajoji. Bangarorin biyu sun amince da ci gaba da tuntubar juna. (Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp