Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta sanar a jiya Juma’a cewa, bisa gayyatar da mataimakin firaministan kasar Singapore Gan Kim Yong ya yi masa, mataimakin firaministan kasar Sin Ding Xuexiang, zai ziyarci kasar Singapore a ranakun 10 da 11 ga watan Nuwamba.
Mao ta ce, Ding da Gan za su jagoranci taron majalisar hadin gwiwa tsakanin Sin da Singapore karo na 20, da taro karo na 25 na majalisar hadin gwiwar gudanarwa na Sin da Singapore (JSC) na yankin masana’antun Suzhou, da taro karo na 16 na majalisar hadin gwiwar Sin da Singapore kan yankin kiyaye muhalli na Tianjin Eco-City JSC, da taro karo na 8 na majalisar hadin gwiwar Sin da Singapore na Chongqing kan shirin gwaji na Sin da Singapore bisa manyan tsare-tsare.
Hakazalika, bisa gayyatar da shugaban kasar Azerbaijan Ilham Aliyev ya yi masa, Ding, a matsayin wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai kai ziyara kasar Azerbaijan, domin halartar taron kolin shugabannin kasa da kasa kan daukar matakan daidaita sauyin yanayi da za a yi a ranakun 12 da 13 ga watan Nuwamba, inda ta kara da cewa, Ding zai ziyarci kasar Azerbaijan bisa gayyatar da mataimakin firaministan kasar Azerbaijan Shahin Abdulla oglu Mustafayev ya yi masa. (Yahaya)