Mataimakin firaministan kasar Sin, kana jagoran tawagar kasar mai tattauna batutuwan tattalin arziki da cinikayya da tsagin Amurka He Lifeng, ya zanta ta kafar bidiyo da sakataren baitul-malin Amurka Scott Bessent, da wakilin cinikayyar kasar Jamieson Greer a jiya Asabar.
Yayin zantawar tasu, jami’an sassan biyu sun amince da gudanar da sabon zagayen tattaunawa game da batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya nan ba da jimawa ba.
Kazalika, sassan biyu sun yi musayar ra’ayoyi bisa sahihanci, da zurfafa tattaunawa, da musaya mai ma’ana dangane da yadda za a aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, yayin tattaunawarsu ta wayar tarho a farkon shekarar nan, da ma muhimman batutuwa masu nasaba da dangantakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninsu. (Saminu Alhassan)














