Bisa umarnin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, Mataimakinsa Kashim Shettima zai wakilci Nijeriya a bikin rantsar da shugaban ƙasa mai jiran gado na Gabon, Brice Clotaire Oligui Nguema, a Libreville a yau.
Oligui Nguema, wanda ya taɓa rike muƙamin shugaban riƙon ƙwarya tun a watan Agusta 2023, ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga Afrilu da gagarumin rinjaye, inda ya samu kashi 94.85% na yawan ƙuri’un da aka kaɗa (ƙuri’u 58,074) kamar yadda Kotun Tsarin Mulki ta Gabon ta tabbatar.
- Shettima Ya Gayyaci Shugaban NAHCON Da Mambobin Hukumar Kan Shirye-shiryen Hajjin 2025
- Masu Sa Hotona A Soshiyal Midiya Suna Yabo Babu Abin Da Za Su Samu – Hadiza Gabon
Ya doke ‘yan takara bakwai, ciki har da tsohon Firayim Minista Alain Claude Bilie-By-Nze, wanda ya zo na biyu da kashi 3% kacal na yawan ƙuri’un.
Halartar Nijeriya tana nuna goyon bayanta ga tsarin dimokuraɗiyya da kwanciyar hankula a yankin Afrika ta tsakiya. Nijeriya ta kuma jaddada sha’awarta ta ci gaba da inganta zaman lafiya a nahiyar.
Ana sa ran Mataimakin Shugaban Ƙasa zai komo Nijeriya nan da nan bayan bikin. Taron na cikin manufofin ketare na Najeriya na kara karfin dangantaka da kasashen Afirka.