Jarumar Kannywood Hadiza Aliyu ko kuma Hadiza Gabon kamar yadda akafi saninta ta bayyana cewar a wannan lokacin da kafafen sada zumunta suka yi yawa a Nijeriya kuma matasa da dama suke amfani da ita, wasu daga cikin matasan sukan yi amfani da wannan damar su dinga dora hotunan wasu mutane musamman ‘yan kasuwa, yan siyasa da sauran masu hannu da shuni a shafukansu suna yabon su.
Wannan yabo ko kirari da fatan alheri da suke yi wa wadanda suka dora a shafukansu ba suna yi ne domin Allah ba, suna yi ne domin kawai wadannan mutanen su dinga samar masu wani dan ihisani na kudi suna basu, amma ita kam duk wanda ya dora hoton ta saboda kawai ya samu wani abu daga gareta kawai ya na wahalar banza ne domin kuwa babu abinda zai samu a wajenta.
- Tsohuwar Jarumar Kannywood Fati Slow Ta Rasu
- Fina-finai Masu Dogon Zango Koma Baya Ne Ga Masana’antar Kannywood – Tanimu Akawu
Jarumar ta ci gaba da cewar idan wani ya na neman wata bukata a wajenka zai fara dora hotunan ka yana yi maka kirari da sauran dadadan maganganu saboda bayan kwana biyu da yin wannan rubutun zai iske ka har gida ya fada maka bukatocinsa, kai kuma saboda ka ga wannan yabon da ya yi maka a kafar sada zumunta zai sa ka yi mashi wani abu da zai magance ma shi matsala ko da ace ba ka biya masa gaba daya ba.
Gabon ta ce a duk lokacin da wani ko wata ya ga anyi posting din hotunan shi kokuma wasu ayyuka da yake gudanarwa ana yabon shi to ya sani ba don Allah ake yi ba,kana zaune a gidanka zai zo ya ce ga bukatarshi ta kudi, karatu, lafiya ko kuma wata bukatar daban, saboda haka ku sani muddin ka daina bayar da kudi ga irin wadannan mutane masu irin wadannan halaye to kai kuwa ba za a sake dora hotonka ana yabonka a soshiyal midiya ba.