Mataimakin Shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima a ranar Asabar ya buɗe sabon gidan Gwamnatin Jihar Bauchi da gwamnatin Gwamna Bala Muhammad ta gina domin saukaka aiki da kyautata harkokin mulki.
Da ya ke jawabi a wajen taron, Shettima ya jinjinawa irin tunanin Gwamna Bala wajen ganin ya sabunta jihar, ya kuma yi kira ga Gwamnonin Arewa maso gabas da su maida hankali wajen ganin sun gudanar da kyawawan ayyukan da za su kai ga taimaka wa shiyyar.
- Al’adu Masu Ban Al’ajabi Da Suka Ki Bacewa Duk Da Sauyin Zamani A Afirka
- Ana Zargin Wani Hadimin ‘Yar Majalisa Da Yi Wa Almajiri Fyade A Kaduna
Ya na mai cewa, “Tabbas Gwamnonin Arewa maso gabas su na matukar kokari wajen kyautata mulki”, sai ya kirasu da su kara azama wajen kyautata rayuwar jama’arsu.
Shettima ya taya Gwamna da al’ummar Bauchi murnar samun sabon Gidan Gwamnatin da zamanantar da shi domin saukaka aiki, ya kuma yaba wa gwamnan kan ayyukan raya birane da karkara.
Tun da farko a jawabinsa, Bala Muhammad ya nuna matukar farin cikinsa a bisa amsar gayyatarsu da mataimakin Shugaban kasan ya yi, ya ce, aikin zamanantar da fadar Gwamnatin Jihar na daga cikin mafarkan da ya jima ya na yi wajen ganin ya kyautata rayuwar al’umma.
Bala Muhammad ya kuma tabbatar da cewa, zai cigaba da zage damtse wajen ganin tattalin arziki ya ci gaba da bunkasuwa a Jihar, sai ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da al’ummar jihar da su ci gaba da bai wa gwamnatinsa da sauran Gwamnonin Arewa maso gabas goyon baya domin tabbatar da ci gaban yankin.
Daga cikin wadanda suka kasance a wajen kaddamar da fadar har da kungiyar Gwamnonin Arewa maso gabas; Tsohon Gwamnan Bauchi a zamanin mulkin soja, Manjo-janar Abutu Garuba; Tsoffin Gwamnonin Jihar, Alhaji Ahmed Adamu Muazu, Muhammad Abubakar, da sanatoci da ‘yan majalisu da sauran su.