Shugaban Kasar Gambia, Adama Barrow, ya sanar da rasuwar mataimakin shugaban kasar, Badara Alieu Joof, a wani asibitin Indiya bayan gajeruwar rashin lafiya.
A cewar majiyoyi daga kasar, hukumomin kasar na shirin gudanar da jana’izar fitaccen dan siyasar kuma tsohon ma’aikacin gwamnatin kasar.
- Idan Aka Zabi Atiku Zai Jefa ‘Yan Nijeriya Cikin Yunwa, Zai Sayar Da Komai – Tinubu
- Kasar Sin Na Samun Bunkasuwa Mafi Girma A Duniya
Badara Alieu Joof ya shahara sosai a harkokin siyasar kasar.
Talla
Ya kasance tsohon ma’aikacin gwamnati, wanda ya taba rike mukamin mataimakin shugaban kasar tun shekarar 2022 har zuwa rasuwarsa.
Ya taba rike mukamin Ministan Ilimi mai zurfi, Bincike da Fasaha daga 2017 zuwa 2022.
Talla