Bisa gayyatar da aka yi masa, mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya halarci nadin sarautar sarki Charles III, wanda aka gudanar da bikin nadin sa a masarautar Birtaniya a hukumance.
Han ya halarci shagulgulan nadin sarautar ne a ranaikun Juma’a da jiya Asabar, a matsayin wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, inda ya gabatar da sakon matukar murnar shugaba Xi ga sarki Charles III, tare da yiwa sarkin da mai dakin sa gimbiya Camilla, da ma sauran iyalan gidan sarautar, da daukacin al’ummar Birtaniya fatan alheri.
Da yake mayar da jawabi game da sakon na shugaba Xi, sarki Charles III, ya bukaci Han da ya mika matukar godiyar sa, da gaisuwar girmamawa ga shugaba Xi, da uwar gidan sa farfesa Peng Liyuan, bisa sakon da suka aika masa, da gimbiya Camilla, na murna da fatan alheri.
Sarki Charles III ya kara da cewa, alakar Sin da Birtaniya na da matukar muhimmanci, yana kuma fatan kasashen 2 za su ci gaba da zurfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban, kamar na rage fitar da abubuwa masu dumama yanayi da iskar Carbon, da fannin wanzar da ci gaba mai dorewa, da dakile sauyin yanayi.
A hannu guda kuma, ya yi fatan Sin za ta ci gaba da taka rawar gani wajen ingiza manufofin samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da sauran muhimman fannoni. (Saminu Alhassan)