Akwai matutar muhimmanci ga mai kiwon kajin gidan gona ya san yadda zai hada abincin kajinsa da kansa musamman masu kiwon Kajin gidan gona masu saurin girma da ake kira a Turanci, da broilers.
Masara:
Za a sami masara kilo 50 sai a hada ta da abinci kilo 100 na buhu hudu ke nan ko kuma kilo 25 ga wanda zai hada buhu 2, kawai dai duk adadin da mutum zai hadd zai iya samun adadin da ya yi daidai da jadawalin wannan kiyasi wato kari daga kan kilo 50 zuwa sama ko zuwa kkasa adadin dai kawai shine a raba gida biyu ko ninkawa gida biyu misali abinci buhu biyu ana bukatar masara kilo 25 , buhu daya kuma masara kilo 12.5. amma kafin a auna adadin da za ayi amfani da ita sai a kai inji a nukata kamar yadda ake bukatata sai a yi nikan ya yi dan laush.
Waken suya:
Anan za a sami waken suya kilo 10 ga wanda zai hada buhu hudu kilo 100, kilo 5 ga mai hada buhu 2, kilo 2.5 ga mai hada buhu 1, amma ana bukatar waken ya kasance an nika shi kar yadda aka yi bayani a masara kafin a auna ko ahada da sauran kayan hadin, kafin a nika a soya shi kadan domin kone waddansu sinadarai dake kawo rashin saurin narka abinci a cikin kaji.
Yanda za a soya shi kuma za a nemo yashi a zuba a cikin tukunya ko kwanon suya babba a dora akan wuta a rika juyawa bayan yashin ya danyi zafi a zuba waken suyar a ciki a rika juyawa akai akai har zuwa dan wani lokaci misalin mintuna 5 har zuwa 20 idan bai soyu ba ya dai danganta da yanayin zafin wutar da aka rura take, amma anan ina son mai wannan suya kada ya bari waken suyar ya kone da yawa don idan ya kone dayawa babu wani amfani da zai yi saboda za a kone harda masu amfanin da ake bukata don haka idan za ayi suyar a soya kamar yadda ake soya Gyada
Kwakwar Manja:
Kuli-kuli:
Ana samunsa kamar yadda yake a hoton da yake kasa.Idan abincin buhu 4 za ayi sai a yi amfani da kilo 12Â ne kawai, idan kuma buhu 2 ne da kilo 6 Kwakwar za a yi amfani, haka kuma ga wanda zai yi buhu 1 sai yayi amfani da kilo 3 a hada.
Oyster shell :
Wannan ana amfani da shi ne idan dusar finisher za a hada domin yana dauke da calcium sosai wanda ke sakawa kaji kkarfin kashi wanda zai taimakawa kajin samun karfin jiki dana kafafunsu.
Ana son abincin da za hada ya kai kilo 100kilo ne wato buhu 4 kenan ana amfani da kilo 1 ne na Oyster shell, idan kuma buhu 2 ne kilo 0.5 za a saka, kilo 0.25 a buhu 1.
Bone meal ko fish meal:
Sai Bone meal ko fish meal ga wanda zai hada kilo 100, buhu 4 zai yi amfani da 3kg na Bone meal ko fish meal wato a buhu 4 kenan, idan kuma kilo 50 ne buhu 2 za’ayi amfani da kilo 1.5 0.75 ga wanda zai hada buhu 1 kilo 25.
Sandarin Bitamins da na Minerals Premid:
Wannan shi kuma za a zuba kilo 0.25 a buhu 4, kilo 0.125 a buhu 2, 0.kilo 062Â a buhu 1.
Methionine:
Za a zuba kilo 0.3 a buhu 4 kilo 100 ds kilo 0.15Â a buhu 2 sai kilo 50 da kilo 0.75Â a buhu 1 na kilo 25.
Lysine:
Wannan shi kuma za a zuba kilo 0.25kg a buhu 4, kilo 0.125 a buhu 2, 0.sai kuma kilo 0625Â a buhu 1.
Gishiri:
Wannan ana amfani dashi dan kadan, kilo 0.2 a buhu 4 kilo 100, kilo 0.1Â a buhu 2, kilo 50 , kilo 0.05 a buhu 1 kilo 25 .
Gishiri yana da matukar amfani a cikin sinadaran hada abincin kaji domin idan yayi karanci matsala ce, saboda mafi yawancin abincin kaji idan kuka ga yaki saka kaji girma zai iya yiyuwa tun a kamfani aka sami matsala wajen saka gishiri saboda gishiri yana budewa kaji ciki suci abinci,yana kuma saita yanayin jikin kaji yana kuma aikin bada kariya wajen halittu masu hadari a cikin kaji. Amma yana da kyau a kula idan gishirin yayi yawa yana kawo matsaloli wanda suka hada da mace-macen kaji.