A shekarar da ta gabata ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake farfado da babban kwamitin kiula da tsare-tsaren kasa a kan al’murran da suka shafi masa’anantun sarrafa fatu a Nijeriya da kuma yadda za a tabbatar da samuwar fatun don wadata masa’anantun da kayan aiki, babbar burin shugaba Muhammadu Buhari a na shi ne baya ga farfado masa’anantumu da kuma samar da aikin yi ga dinbim matasanmu da samarwa da kasa kudaden shiga ta hanyar fitar da kayyakin da aka saffara zuwa kasuwannin kasashen waje.
Shugaban Ma’aikatar Kimiyyar Fatu wato (Nigeria Institute of Leather and Science Technology (NILEST) wanda ke Samaru Zaria ta Jihar Kaduna, Farfesa Mauhammad Kabir Yakubu shi ne aka ba alhakin jagorantar wannan kwamiti (National Leather Policy), wanda ta kunshi dukkan masu ruwa da tsaki a bangaren abubuwan da suka shafi sarrafa Fatu a Nijeriya.
A tattaunawarsa da Mataimakin Editanmu Bello Hamza ya bayyana mana yadda wananan hankoro na Shugaba Buhari ya ke haifar da da mai ido, yana Magana ne bayan taron da ya halarta na masu ruwa da tsaki a kan harkokin da suka shafi bunkasa masa’nantun fatu a Nijeriya da aka yi a Legas ranar Litinin 27 ga watan Satumba 22.
Yadda Tafiyar Ta Faro…
A matsayina na DG kuma shugaban wannan ma’aikata ya kuma kara mani wani nauyi saboda akwai wani ‘Policy’ na gwamnati wanda yake an bata wato aikin sannin yadda za ta farfado da aikin wato masana’antun fata da kuma masana’antun da ke maida fata ta zama wasu abubuwan da ake siyar wa. A cikin wannan policy din wanda yake nan tun wajen 2018, gwamnatin tarayya ta yarda da wannan policy din, sai kuma watan Yuli na shekarar 2021, wanda yake shugaban kasa ya gabatar da kwamiti na zartarwa na wannan ‘Policy’ din. Ya bamu aikin sanin ya za a farfado da masana’antun fata a Nijeriya.
Tun daga lokacin muka dukufa muna tattaunawa da wanda ke da wuka da nama, masu ruwa da tsaki. Mun yi zama a Kano, wanda mun kira duk wasu masu masana’antun jima, da kuma wanda ke sarrafa fata don mayar da su Takalma, Jakar, da sauransu.
A wannan binciken mun fahinci cewa, fatun da ake sarrafawa sun yi karanci kwarai da gaske a Nijeriya, wannan yasa yakamata idan muna so a farfado da wannan sana’ar a Nijeriya ta nan ya kamata mu fara, tunda duk yadda mutumin da yake son ya sarrafa wani al’amari idan bashi da “Raw Materials” ba za a samu cigaba ba. Kuma Allah ya azurta mu da wannan abubuwan da muke sarrafawa.
Akalla a diddigi da akayi muna da shanu akalla sun kai wajen Miliyan Arba’in. Muna da awaki da tumaki sun kai wajen miliyan saba’in, muna da dawakai, muna da jakuna, da rakuma, duk wannan ana iya maida su fatu. Amma matsalan da muke samu yanzu babba, maimakon mu sarrafa wannan fatun sai ya zama mutane suna ci.
Kuma cin bai dame mu ba inda ace shi wanda zai siyo ya sarrafa zai same shi cikin sauki, misali shi wanda yake so ya yi sana’ar jima idan yana sin ya ci riba bai kamata ya siya fata fiye da dubu goma ba, fatar sa. Amma kuma zaku sha mamaki wanda ke siyan shi din su ci suna siyan shi ya kai wajen dubu ashirin da biyar.
Ya fi amma kuma idan aka yi nazarin abin a nan gaba mun cutar da kasa ne. Me yasa na ce haka? Idan ka kai fata saboda a jeme shi ya zama fatar gaske, akwai wasu abubuwa da ake yi tun daga lokacin da aka cire fata din, aka fede fata din. Akwai abun da ake kira “Preserbation” ana sa mashi gishiri ko wani abu saboda kar ya lalace kafin a kai shi wurin jima din. Idan aka kai shi wurin jima din akwai wasu matakai guda uku muhimmai, ana ce masu “Pre taning” wanda yake abubuwa ne da dama akalla sai ya ratsa mashin wajen hudu.
Sannan akwai jima ita kashin kanta, inda ita wannan taning ake, shima akwai wani ‘process’ wanda yana bukatar mutane da yawa a kan injin din. Sannan akwai abun da ake ce ma “Post Taning” lokacin da za a kara inganta fata din ya kara sa shi ya zama ‘standard’.
Toh kaga duk wadannan ‘process’ din ana bukatar mutane wanda za su yi aiki, kuma mutanen da ake ba in kowanne za ka bashi albashi ne. Toh bayan an yi hakan din ana maida fatan ya zama a wadace ga ‘yan Nijeriya. Toh amma yanzu fatan da ake amfani da ita a wannan masa’ananta din shigo da ita ake yi daga waje, idan aka kwatanta wannan din kuma da wanda ake ci da kaje ka cire fatar ka zuwa za a yi a babbake, mutane nawa ke aikin? Bai wuce dayan biyu ba. Toh kaga kenan shin wanda ke siye don ya kai masana’anta, ba kawai kan shi yake tunani ba yana tunanin wanda zai ba aiki domin sarrafawa. Amma shi kuma wannan ci kawai zai yi, da an debe sai a kai ma wanda zai siya ya siyar.
Ita kuma gwamnati kowani lokaci tana tunanin abun da za ta yi ne don samun ma ‘ƴan kasan ta ayyuka, saboda ayyuka sun yi wa gwamnati yawa. Idan ba mu da kanfuna wanda ke iya samo kudi da zai samar ma mutane aiki a Lokaci daya da yawa sannan kuma a samu kudin da za a iya biyan su shi ma kamfanin ya samu riba. Toh kasar nan za a samu matsala. Me yasa fatar da ake samowa daga waje ta fi ta Nijeriya arha? Dalilin kenan.
Saboda wadancan wuraren basa cin fatan, suna siyanta da arha sai su sarrafa ta cikin arha, ya zo Nijeriya cikin arha har ma ya kasance dan Nijeriya gara ka siya daga waje da ya siya wanda aka sarrafa a Nijeriya. Saboda wurin mutumin nan ya yi tsada da yawa. Toh wannan sune hujjojin da muka ga yakamata lallai a kawo wani doka wanda za ta haramta ma mutane cin fata dinnan.
Kai a manta da wannan ma, idan kabi wajen harkar kimiyya, yadda ake sarrafa fata din ita ma akwai matsala, ana amfani da tayoyi ne a babbaka fata. Hatta anfani da taya ma an hana, ka babbaka taya, saboda akwai wani sinadari da ke shiga yana cutar da mutane. Kuma duk yadda kayi bar badin wannan sinadarin yana shiga jikin mutane.
Bani da tabbas amma akwai kimiyya wanda ya nuna yawan kansa da mutane ke samu yana da alaka da wannan abun da ake ci.
Bukatar Samar Da Kayan Sarrafawa A Masana’antun Fatu A Nijeriya…
Toh in dai maganan batun al’ada ina tsammanin duk a Nijeriya babu wanda baya cin fata. Tun ina yaro yanzu wajen shekara Hamsin nake dashi nasan akwai wai abu da ake ce ma “Langaɓu” ni ba sakkwace ne mun saba muna cin fata. Ana maganan abun da zai zama anafani ga kasa ne baki daya. Sannan kuma ina bada hakuri, abun kunya ne a duniya ace babu inda ake cin fatan dabba sai ƴan Nijeriya.
Duk da Mutanen Chinese basa wasa da nama ni ban taba jin inda aka ce mutanen Chana na cin fata ba. Alhali babu abin da basu ci, amma fata dai ita wannan an yi tane don a sarrafa ta. Ina ganin wannan dai shikenan.
A gaskiya daga 1990 zuwa 2000, muna da masana’antun sarrafa fata wato majema kenan da suka kai wajen arba’in da hudu.
Wanda yake a lokacin abin da ake samu a sarrafa fata, locacin fata ake kai wa waje, ya kai wajen miliyan 800. Alhali kuwa mu abin da muke tsammani, muna so ya zama zuwa 2025, ya zama abin da za a iya samo wa kasa wajen sarrafa fata da sauran abubuwa.
Muna so ya kai akalla Dala Biliyan daya. Idan na dawo tambayar ka ka maida fatun ake sarrafawa a Nijeriya kawai saboda sarrafa ta a kanfuna cikin karamin lokaci za su dawo da aiki. Shi masana’anta na Jima ba masana’anta ce wanda ke bukatar mutane da yawa ba kamar masana’anar masaku ba ne (Tedtile). dan karamin waje zaka ga abin da za a fitar sai ka sha mamaki.
Mashina ba zai wuce guda ashirin ba amma za a iya sarrafa kamar Tan daya ko tan biyu a cikin lokaci daya.
Matakan Tabbatar Da Kafa Dokar Hana Cin Fata…
Toh dama ita hanyar kawo kudiri a majalisa dama sannannu ne, mu a matsayinmu na masu ruwa da tsaki a cikin wannan al’amari mu zamu kai ma majalisa sai mu samu wanda zai gabagtar da ita ga majalisa.
Yadda dai ake yi a kira mutane a fada abin da ake so ayi kafin daga baya ya zama doka.
Har shugaban kasa ya sa hannu. Amma an taba gabagtar da irin wannan dokar a lokacoin baya, abin ya dakata, toh mu sake dawo da ita Insha Allahu ba wani babban abu ba ne. Amma hanyar da ake bi saboda a kai wani doka, hanyoyin da ake dauka kafin ya zama doka duk sannannu ne, kuma gaskiya muna son ne mu fara daga jiha.
Mu je jihohi mu gaya masu, inda wannan abin yafi kamari. Wanda ke saye da siyar wa a hana masu wannan fata din. Sannan kuma ina so in ba su masu fata din hakuri.
Kila suka cewa za su yi asara, toh Insha Allahu zamu samo wasu hanyoyi wanda zai sa mu dinga siyan fata din yadda ba za su yi asara ba. Idan suna wasu masana’antun suna siyan shi ko dubu goma ko abi da ya fi haka, to inshaAllahu za mu shigo, a san yadda za a yi a samu wato matsayar da kai dai baka yi asara ba. Kuma duk abin da ake so a samu na anfanar da kasa an samu kuma kasa ta anfana.
NILEST Za Ta Jagoranci Gudanar Da Binciken Kimiyya Don Bunkasa Bangaren…
Wato mu a nan muna da bangaren guda uku ne, wato akwai Research, akwai Training akwai kuma abin da ake ce ma Community serbice. Toh mafi yawancin bangarorin da muke dasu, bangaren bincike wato ‘Research’ yakan zo mana da matsala saboda akwai bukatar kudi.
Toh abin da na yi kokari da na zo shi ne in kirkiro kuma in sanya mutane cikin kungiyoyi saboda su kawo wasu tunanin su na abin da zaaa kawo na bincike domin cigaban wannan ma’aikata da masana’anta, wato masana’antun. Toh mun samu wasu kungiyoyi kaman guda goma sha uku wanda sun kawo ayyuka wanda suka shafi sinadarin da ake yin jima dashi. Sannan kuma da sinadarin da ake inganta fata.
Sannan da sinadarin da za a iya sa wa fata wanda ba zai lalace ba har ya kai inda za a sarrafa wato kamfani. Da ana anfani da gishiri ne, toh gishiri yana da matsala saboda yana bata muhalli.
Sannan kuma sai na’urori akwai kananan abubuwa da ake yi wajen sarrafa fata da kanta wanda ba sai mun dinga shigowa dashi daga waje ba.
Toh mun kirkiro wadannan kusan guda goma sha uku, toh Alhamdulillah yanzu haka nan gaba zamu kira wani taro cikin watan Disasmba zamu kira al’umma su zo su ga abubuwan da aka cimma a cikin karamin lokaci, a cikin shekara biyu. Mun kashe abin da ya kai wajen miliyan dari.