• English
  • Business News
Wednesday, August 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matakan Sin Na Yaki Da COVID-19 Sun Haifar Da Da Mai Ido

by CMG Hausa
3 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Matakan Sin Na Yaki Da COVID-19 Sun Haifar Da Da Mai Ido
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Cibiyar yada shirye-shirye da harsunan Asiya da Afrika, na Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ya gudanar da wani taron karawa juna sani kan yanayin kasar Sin a kokarinta na dakile cutar COVID-19.

Idan ba a manta ba, kasar Sin ce kasa ta farko da ta sanar da bullar cutar a hukumance ga hukumar lafiya ta duniya a karshen shekarar 2019, duk da cewa, sakamakon tarin bincike sun nuna cewa, an samu bullar cutar a wurare da dama kafin a same ta a kasar Sin. Baya ga haka, har kawo yanzu, babu wata kasa da ta taka rawar gani wajen yaki da cutar kamar kasar ta Sin.

  • Xi Jinping Ya Taya Murnar Gudanar Da “Bikin Nuna Al’adun Larabawa”

Wasu kafafen yada labarai na yammacin duniya da ma gwamnatocinsu, sun yi ta yada jita-jitar cewa, matakan kasar Sin sun take hakkokin bil adama.

Sai dai akasin abun da suke nufi, matakan kasar Sin sun cancanci jinjina matuka, domin sun taka rawar gani wajen kare al’umma daga rasa rayukansu sanadiyyar kamuwa da cutar, haka kuma sun kare yaduwar cutar daga kasar zuwa sauran sassan duniya. Gani ya kori ji, domin duk wani dake kasar Sin zai bada shaidar cewa, matakan sun taka rawar gani. Idan kuma aka duba su kasashen masu yada jita jitar, har yanzu ba su kama kafar Sin wajen yaki da cutar ba, haka kuma suna fama da matsalolin tattalin arziki.

Yadda CMG ya shirya wannan taro, hakika zai kara wayar da kan al’ummomin Afrika kan illolin dake tattare da annobar da ma yadda za su kare kawunansu, da kuma dalilan Sin din na daukar matakan da ta dauka, tare da wayar musu da kai daga karai-rayi ko jita-jita da aka yi ta yadawa dangane da su. Baya ga haka, zai zama darasi ta yadda gwamnatocin kasashen za su iya shiryawa tunkarar annoba da mai yuwuwa ka iya barkewa a nan gaba.

Labarai Masu Nasaba

Sin Na Goyon Bayan Duk Wani Mataki Na Warware Batun Ukraine Ta Hanyar Lumana

Ilimin Fasahar Zamani Dama Ce Ta Samun Kyakkyawar Makoma A Afrika

Duk da cewa, ana ganin Sin ta dauki tsauraran matakai, matakan nata sun haifar da da-mai-ido, ta cimma dimbin nasarori, domin ita ce kasa daya tilo da ta samu ci gaban tattalin arziki bayan bullar annobar, haka kuma ita ce ta bayar da gudunmawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya.

Haka zalika, wadannan kyawawan manufofi ne ya sa ake ganin yayin da ci gaban kasashen duniya zai gamu da cikas a shekarar 2023, an yi hasashen tattalin arzikin kasar Sin zai farfado tare da kara kuzari. Ingantattun manufofin kudi da Sin ta dauka da kuma saukaka matakan yaki da annobar da ta yi a baya-bayan nan, za su taimaka wajen samun habakar tattalin arzikinta wanda zai ci gaba da bayar da gudunmawa ga tattalin arzikin duniya baki daya. Haka kuma, zai kara bunkasa harkokin cinikayya da mu’amala da ma musaya da kasashe masu tasowa aminanta, musammam ma na Afrika.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Shugaban Kasar Sin Ya Tattauna Da Takwaransa Na Cote d’Ivoire

Next Post

Sinawa Suna Tinkarar COVID-19 Da Karfin Gwiwa

Related

Sin Na Goyon Bayan Duk Wani Mataki Na Warware Batun Ukraine Ta Hanyar Lumana
Daga Birnin Sin

Sin Na Goyon Bayan Duk Wani Mataki Na Warware Batun Ukraine Ta Hanyar Lumana

13 hours ago
Ilimin Fasahar Zamani Dama Ce Ta Samun Kyakkyawar Makoma A Afrika
Daga Birnin Sin

Ilimin Fasahar Zamani Dama Ce Ta Samun Kyakkyawar Makoma A Afrika

14 hours ago
Sin Ta Ware Yuan Miliyan 170 Domin Ayyukan Tallafi Ga Sassan Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa
Daga Birnin Sin

Sin Ta Ware Yuan Miliyan 170 Domin Ayyukan Tallafi Ga Sassan Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa

15 hours ago
Xi: Sin Da Brazil Na Iya Zama Misalin Hadin Kai Da Dogaro Da Kai Ga Kasashe Masu Tasowa
Daga Birnin Sin

Xi: Sin Da Brazil Na Iya Zama Misalin Hadin Kai Da Dogaro Da Kai Ga Kasashe Masu Tasowa

16 hours ago
Ma’aikatar Cinikayya Ta Kasar Sin Ta Yi Karin Haske Kan Batun Saka Wasu Sassa Cikin Wadanda Ta Sanyawa Takunkumin Sayar Musu Da Kayayyaki
Daga Birnin Sin

Ma’aikatar Cinikayya Ta Kasar Sin Ta Yi Karin Haske Kan Batun Saka Wasu Sassa Cikin Wadanda Ta Sanyawa Takunkumin Sayar Musu Da Kayayyaki

17 hours ago
Sin Ta Gabatar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakaninta Da Amurka A Stockholm
Daga Birnin Sin

Sin Ta Gabatar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakaninta Da Amurka A Stockholm

18 hours ago
Next Post
Sinawa Suna Tinkarar COVID-19 Da Karfin Gwiwa

Sinawa Suna Tinkarar COVID-19 Da Karfin Gwiwa

LABARAI MASU NASABA

ADC Ta Dakatar Da Shugabanta Da Wasu Jiga-jigai 3 A Kebbi

ADC Ta Dakatar Da Shugabanta Da Wasu Jiga-jigai 3 A Kebbi

August 13, 2025
An Kama Hakimi Kan Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 12 Fyaɗe A Gombe

An Kama Hakimi Kan Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 12 Fyaɗe A Gombe

August 13, 2025
PDP Ta Soki Gwamnatin Tinubu Kan Tsare Tambuwal Da EFCC Ta Yi

Tambuwal: ’Yan Nijeriya Sun Soki EFCC Kan Rashin Kama Okowa, Ganduje Da Yahaya Bello

August 13, 2025
Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika Karo Na 12

Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Man Fetur Zuwa N820 Kan Kowace Lita

August 13, 2025
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

‘Yansanda Sun Fara Bincike Kan Rasuwar Wani Dan NYSC A Bauchi

August 12, 2025
Sin Na Goyon Bayan Duk Wani Mataki Na Warware Batun Ukraine Ta Hanyar Lumana

Sin Na Goyon Bayan Duk Wani Mataki Na Warware Batun Ukraine Ta Hanyar Lumana

August 12, 2025
EFCC Ta Bayar Da Belin Tambuwal, Ta Yi Allah-wadai Da Zargin Da Jam’iyar ADC Ta Yi

EFCC Ta Bayar Da Belin Tambuwal, Ta Yi Allah-wadai Da Zargin Da Jam’iyar ADC Ta Yi

August 12, 2025
Babu Neman Afuwa Kan Nuna Goyan Bayan Tinubu Da Na Yi – Soludo

Babu Neman Afuwa Kan Nuna Goyan Bayan Tinubu Da Na Yi – Soludo

August 12, 2025
Ilimin Fasahar Zamani Dama Ce Ta Samun Kyakkyawar Makoma A Afrika

Ilimin Fasahar Zamani Dama Ce Ta Samun Kyakkyawar Makoma A Afrika

August 12, 2025
Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci Sun Kashe Wani Mutum Da Jikkata Wasu Da Dama A Sokoto

August 12, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.