ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, June 26, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sinawa Suna Tinkarar COVID-19 Da Karfin Gwiwa

by CMG Hausa
4 years ago
COVID-19

Wasu abokai sun rubuta mana sakonni a kwanan baya, inda suka tambaye ni kan yanayin da ake ciki a nan kasar Sin, a fannin tinkarar cutar COVID-19. Amsa ita ce, wata sabuwar barkewar cutar nau’in Omicron ta haifar da wasu matsaloli, sai dai ba ta girgiza karfin gwiwar Sinawa ba.

A yayin barkewar nau’in Omicron ta wannan karo, birnin Beijing, inda nake zaune, yana daga cikin wuraren da suka fi fama da yaduwar annobar. Wasu makwabta da abokaina da yawa sun kamu da ita, inda suka fara zazzabi da tari. Ko da yake galibin mutanen da suka kamu da cutar, alamun da suka nuna ba su da tsanani. Amma saboda dimbin mutanen da suka kamu da cutar ake samu a lokaci guda, ya sa an samu cukuson mutane a asibitoci, da karancin wasu magunguna a shagunan sayar da magani.

  • Sin Ta Sha Alwashin Kare Hakkokinta A Gabar Da Amurka Ta Sake Kakabawa Karin Kamfanonin Sin Takunkumi

Ban da wannan kuma, don magance yin cudanya da mutane masu dauke da kwayoyin cutar COVID-19, jama’a sun daina zuwa sayen kayayyakin abinci da na masarufi a kasuwanni, maimakon haka, sun karkata ga shafukan sayar da kayayyaki na yanar gizo ta Internet gaba daya, lamarin da ya sa ake fuskantar matsalar karancin ma’aikatan jigilar kaya. Don haka yanzu a kan jira karin wasu kwanaki, kafin a iya samun kayan da aka saya ko oda.

ADVERTISEMENT

To, wadannan su ne matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu. Sai dai Sinawa ba su damu sosai ba, ganin yadda suka fara daukar wasu matakai don tinakarar matsalolin. Misali, an bude wuraren ganin likita na wucin gadi, don biyan bukatar mutanen da suke neman ganin likita. Kana an kayyade yawan magunguna da za a iya saya a lokaci guda, ta yadda kowa zai iya samun maganin da yake bukata cikin gaggawa. Ban da wannan kuma, an tura karin ma’aikatan jigilar kayayyaki zuwa wuraren da suka fi fama da annoba, da sanya galibin mutane yin aiki daga gida don magance duk wata kafa ta yaduwar cuta, da lallashin mutane don su huta a gida maimakon zuwa asibiti, idan alamunsu ba su da tsanani.

To, tambaya ita ce, me ya sa Sinawa basa damuwa, ko da yake cutar COVID-19 na yaduwa cikin sauri?

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji

Saboda sun san matsalar ba za ta dade ba, musamman ma a fannin tattalin arziki. Cikin shekaru 3 da suka wuce, kasar Sin ta yi kokarin daukar tsauraran matakai na hana yaduwar cutar COVID-19, kamar takaita zirga-zirga, da umartar ‘yan kasa don yin gwaji, da killace wadanda suka kamu da cutar har zuwa lokacin da suka warke, da dai sauransu, don kare lafiyar jama’ar kasar, ko da yake matakan na haifar da matsi a fannin tattalin arizki. Amma duk da haka, matakan ba su hana ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ba, inda matsakaiciyar karuwar GDPn kasar cikin wadannan shekaru 3 ta kai kashi 4.6%, gaba da na sauran manyan kasashe irinsu Amurka, da Japan, da Jamus, da Faransa. Sa’an nan zuwa wannan lokacin da muke ciki, kasar Sin ta daidaita manufarta ta kandagarkin yaduwar cuta, inda ta sassauta wasu matakan kayyadewa, bisa la’akari da sabon yanayin da aikin tinkarar cutar ke ciki. Hakan ya sa ‘yan kasar ke sa ran ganin karuwar tattalin arizkin Sin cikin karin sauri, bayan da yanayin bazuwar nau’in Omicron na cutar na wannan karo ya kai karshe.

Sa’an nan, wani dalili na daban da ya kawar da damuwar Sinawa, shi ne amincewarsu kan gwamnatin kasar. Sun fahimci dabarar gwamnatin a fannin tsara manufofi: Ta kan tsara wata manufa bisa hakikanin yanayin da kasar ke ciki, da kokarin daidaita manufar a kai a kai, bisa sauyawar sharadi. Ganin yadda kasar Sin ke da tsoffin da yawansu ya kai fiye da kashi 17% na yawan al’ummarta, wadanda kuma suka fi fuskantar hadari idan sun kamu da cutar COVID-19, ya sa kasar daukar tsauraran matakai na dakile cutar cikin shekaru 3 da suka wuce. Sa’an nan zuwa yanzu, yadda fiye da kashi 91% na tsoffin kasar suka riga suka karbi allurar rigakafin cutar, da yadda karfin yaduwar cutar nau’in Omicron ke karuwa, amma kuma karfinta na haddasa mutuwa ke raguwa, sun sa gwamnatin kasar Sin samun damar daidaita manufarta ta kandagarkin cutar.

Duk wata manufa da aka dauka a kasar Sin, jama’ar kasar na da cikakken karfin gwiwa kan cewar, gwamnati za ta kare moriyar daukacin al’ummar kasar, bisa akidarta ta kokarin bautawa jama’a. (Bello Wang)

COVID-19
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

June 25, 2026
Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji
Daga Birnin Sin

Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji

June 25, 2026
Shugabar Namibia Ta Kaddamar Da Dakin Baje Kolin Kimiyya Da Sinawa Suka Gina
Daga Birnin Sin

Shugabar Namibia Ta Kaddamar Da Dakin Baje Kolin Kimiyya Da Sinawa Suka Gina

June 25, 2026
Next Post
Hisbah Ta Cafke Samari Da ‘Yanmata 19 Wurin Auren Luwadi A Kano

Hisbah Ta Cafke Samari Da 'Yanmata 19 Wurin Auren Luwadi A Kano

LABARAI MASU NASABA

Birtaniya Da Nijeriya Sun Ƙulla Yarjejeniya Kan Yaƙi Da Ta’addanci

Birtaniya Da Nijeriya Sun Ƙulla Yarjejeniya Kan Yaƙi Da Ta’addanci

June 26, 2026
Rashin Tsaro: Ana Ƙoƙarin Ganin Ƙarshen Haƙurin Arewa – ACF

ACF Ta Ƙaddamar Da Gidauniyar Tallafa Wa Ilimi A Arewa

June 26, 2026
Damunar Bana: Yadda Gwamnati Da Manoma Ke Tunkarar Barazanar Ƴan Ta’adda

Damunar Bana: Yadda Gwamnati Da Manoma Ke Tunkarar Barazanar Ƴan Ta’adda

June 26, 2026
Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

June 25, 2026
Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji

Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji

June 25, 2026
Shugabar Namibia Ta Kaddamar Da Dakin Baje Kolin Kimiyya Da Sinawa Suka Gina

Shugabar Namibia Ta Kaddamar Da Dakin Baje Kolin Kimiyya Da Sinawa Suka Gina

June 25, 2026
Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Bayar Da Ƙarin Tallafi Ga Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Bayar Da Ƙarin Tallafi Ga Jami’an Tsaro A Zamfara

June 25, 2026
Salon Jagorancin Kasar Sin Na Ingiza Samar Da Ci Gaba Mai Nagarta

Salon Jagorancin Kasar Sin Na Ingiza Samar Da Ci Gaba Mai Nagarta

June 25, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Dangote Ya Rage Farashin Fetur Zuwa N1,125 Kan Kowace Lita

June 25, 2026
Adadin Injunan Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ya Wuce Kilowatts Awa Biliyan 4, Wato Ya Kai Ga Matsayi Na Farko A Duniya

Adadin Injunan Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ya Wuce Kilowatts Awa Biliyan 4, Wato Ya Kai Ga Matsayi Na Farko A Duniya

June 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.