Matakan tilasta bin doka na kashin kai, ya saba doka, kuma ba shi da wata ma’ana, kana wani mummunan bala’i ne ga daukacin bil-Adama, don haka kasar Sin ta bukaci Amurka da wasu kasashen yammacin duniya, da su fuskanci tsarin shari’a na kasa da kasa wajen neman adalci, kana su gaggauta soke irin wadannan matakai, maimamon haka su aiwatar da tsarin hadin gwiwar sassa daban-daban na hakika, da ayyuka a zahiri, kamar yadda mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing ya bayyana a ranar Laraba. (Mai fassaawa: Ibrahim daga CMG Hausa)