Kungiyar masana’antun sarrafa ma’adanan da ba na karfe ba ta kasar Sin, ta ce matakin kasar na karfafa lura da yadda ake fitar da abubuwa masu alaka da ma’adanan “rare earth”, na nuni ga aniyar Sin ta tabbatar da tsaron duniya da wanzar da zaman lafiya.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a jiya Lahadi, bayan da ma’aikatar cinikayya, da babbar hukumar kwastam ta kasar suka sanar da matakin takaita fitar da wasu abubuwa masu alaka da nau’ika 7 na ma’adanan “rare earth” masu matsakaici nauyi da kuma masu nauyi.
- Cin Zali Ba Zai Iya Hana Kasashen Afirka Ci Gaba Ba
- Ya Kamata A Yi Adawa Da Kama Karya A Tabbatar Da Adalci
Kungiyar ta ce ana amfani da abubuwan da ake sarrafawa daga ma’adanan “rare earth” a ayyukan soji da kuma na fararen hula, kuma matakan Sin na takaita fitar da su sun dace da tsarin gudanarwa na kasa da kasa.
Kazalika, a cewar kungiyar, matakin takaita fitar da nau’o’in sinadaran ba zai shafi kamfanoni masu bukatarsu ba, muddin ba sa gudanar da wasu ayyuka daka iya zama illa ga tsaron kasar Sin, da ikon mulkin kan kasar, ko moriyar ci gabanta. Har ila yau, matakan ba za su haifar da cikas ga daidaito da wanzuwar tsarin gudanar da masana’antu na kasa da kasa da na rarraba hajoji zuwa sassan duniya ba. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp