Bayani ya nuna cewa, matan tubabbun ‘yan ta’addan Boko Haram da na ‘yan kungiyar ISWAP da ke zaune a sansanin Hajj Camp da ke Maiduguri babban birnin Jihar Borno sun haifi jarirai 262 a cikin wata 4 kacal da suka gabata.
‘Yan ta’addan dai na rayuwa ne a cikin kananan gidajen da suka gina a cikin sansanin tare da mata da yaransu inda suke gudanar da rayuwa ba tare da wata mastala ba. Ana samun labarin haihuwa a kai kai a tsakanin iyalan tubabban ‘yan ta’addan.
- Jirgin C919 Na Kasar Sin Ya Samu Amincewar Kara Kera Shi
- CMG Ya Lashe Lambobin Yabo 4 Na Watsa Shirye-shirye Na Gasar Wasannin Olympics Ta Beijing 2022
Sansanin Hajj Camp na daya daga cikin sansanin hudu da gwamnati ta gina don killace ‘yan ta’addan da suka mika wuya ga dakarun Nijeriya a fagen fama.
Kididdigar ya nuna cewa, cikin jariran da aka haifa akwai mata 150 da maza 112. A watan Yuli na wannan shekarar an haifi yara 94 a sansanin yayin da aka haifi yara 98 a watan Agusta, an kuma haifi jarirai 60 a watan Satumba yayin da aka haifi jarirai 11 a watan Oktoba, kamar yadda kididdigar hukumar da ke kula da sansanin ta bayyana.
Mai kula da dakin shan maganin sansanin na Hajj Camp, Dakta Mohammed Sale ya sanar da haka a ziyarar da tawagar bincike suna kai masa.
Da aka tambaye shi ko an taba samun mace-macen jarirai ko kuma matsalar da ta shafi haihuwa? Saioya bayyana cewa, ba su taba samun wata matsala ba, kuma duk wani aiki da ya fi karfinsu suna mika shi ne ga babban asibiti jihar mai suna’ Umoru Shehu Specialist Hospital’ ko kuma asibitin koyarswa na jami’ar Maiduguri.
Bayani ya nuna cewa,a daidai ranar 11 ga watan Nuwamba na shekarar 2022, mutanen da ke zaune a sansanin sun kai 14,804, Maza sun kai 5,200 kuma dukkan su mayaka ‘yan ta’adda ne, jami’an tsaro sun kashe ire-irensu da dama a yankin arewa maso gabas suma ‘yan ta’adda sun kashe al’umma da dama a yankin arewa maso gabas da suka hada da Borno, Yobe da Adamawa.
Daga cikin tubabbun ‘yan Boko Haram din da ke a sasanin na Hajj Camp, 3,427 na zaune ne da matansu yayin da 1,773 basa tare da matan su. Akwai matan aure 4,443 a sansanin. Wannan bayan wasu matan da ke zaune a sauran sansani uku da ke a wasu sassan jihar.
Bayani ya kuma nuna cewa akwai yara fiye da 5,170 a sansanin na Hajj Camp, maza 2,691 mata 2,479.
Mai bayar da shawara na musamman ga gwamnan Borno a kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Abdullahi Sabi Ishak (Mai Ritaya) ya bayyana cewa, fiye da tubbbabun mayakan 3,500 ne gwammnati ta mayar dasu a cikin al’umma, suna can sun cigaba da harkokin rayuwarsu.
Ita kuwa Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Borno, Hajiya Zuwaira Gambo, ta bayyana cewa, gwamnati na samarwa tubabbun mayakan magungunan kula da lafiyar kwakwalwa da kuma tallafin bunkasa rayuwarsu, haka kumma ana samu tallafin daga gwamnatin tarayya da wasu kungiyoyi masu bayar da tallafi daga kasashen waje.
A nasa gudummawar, Shehun Borno Dakta Abubakar Umar Garbai ya nuna jin dadinsa ga kokarin jami’an tsaro a yankin, ya ce a halin yanzu babu wani yankin karammar hukuma da ke a hannun mayakan Boko Haram.