Jami’an rundunar ‘yansandan jihar Bauchi, sun cafke tare da tsare wata matar aure ‘yar shekara 24 a duniya, Furera Abubakar da take kauyen Bantu a karamar hukumar Ningi da ke jihar Bauchi bisa zarginta da kashe jariri dan kwanaki hudu a duniya.
A wata sanarwar da kakakin ‘yansandan jihar Bauchi, Sufuritendan Ahmed Muhammad Wakil ya fitar a ranar Talata, ya ce, wacce ake zargin ta kashe jaririn ne kwanaki hudu da haihuwarsa tun ma kafin zuwan ranar da za a rada masa suna.
- Birtaniya Ta Gurfanar Da Diezani A Gaban Kotu Kan Zargin Almundahana
- Ba Za Mu Yi Karya Don Kare Gwamnati ba – Ministan Yada Labarai
A cewarsa, an kai rahoton faruwar lamarin ne ga caji ofis din ‘yansanda da ke Ningi a ranar 19 ga watan Agustan 2023 inda ake shaida musu cewa wani jariri da aka haifa a ranar 15 ga watan Agustan wata mata da ake zargi mai suna Furera Abubakar ta kasheshi a ranar 19 ga Agustan kwanaki uku kafin zuwan ranar da za a rada masa suna.
Binciken ‘yansanda na farko-farko ya nuna cewa wacce ake zargin kishiyace ga mahaifiyar jaririn.
Wakil ya kara da cewa wacce ake zargin ta kutsa kai cikin dakin kishiyar nata dauke da maganin kashe kwari (Gamalin) inda ta shayar da jaririn da shi.
“Maganin da ake zargin ta yi amfani da shi, ya janyo mummunar illa ga lafiya jaririn wanda sannu a hankali rai ya ce ga garinku yaro dai ya rasu,” ya shaida.
Sanarwar ta ce, yanzu haka ‘yansanda suna kan cigaba da zurfafa bincike kuma da zarar suka kammala za su gurfanar da matar a gaban kotu domin fuskantar laifin da ake zarginta da aikatawa.
LEADERSHIP Hausa ta gano cewa matar (wacce ake zargi) tana da diya mace, ta kai ga fusata ne domin kishiyarta ta haifi da na miji bisa dalilin da ita kadai ta sani.