ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shin Japan Biris Za Ta Yi Da Hakkin Al’ummarta Da Na Makwabtaka?

by CMG Hausa
3 years ago
Japan

Abun mamaki da takaici, duk da adawa daga kasashe makwabta har ma da al’ummar kasar da suke zaman mafiya muhimmanci ga kowane kuduri ko manufar gwamnati, har yanzu Japan tana kan bakanta, inda ta sanar a yau Talata cewa, za ta fara zubar da dagwalon nukilya a cikin teku a ranar Alhamis.

Shin Japan ba ta damu da koke da korafin da al’ummarta ke yi ba ne? Al’ummar kasar da kungiyoyi da kamfanonin masunta, sun bayyana matukar adawa da kudurin gwamnatin kasar, amma da alama, al’ummarta ba sa gabanta, illa abun da ta sa a gaba, wanda ka iya illata al’ummar duniya, har ma da toshewa al’ummarta hanyoyinsu na samun kudin shiga.

  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Kalubalanci Japan Da Ta Dakatar Da Shirin Zubar Da Ruwan Dagwalon Nukiliya Cikin Teku

Su ma al’ummar Koriya ta kudu ba a bar su a baya ba wajen yi zanga-zangar adawa da wannan mataki, a matsayinsu na makwabta da suka fi fuskantar barazanar illar matakin Japan, amma gwamnatinsu ta ki goya musu baya. Shin mene ne amfani gwamnati idan ba za ta tsaya ta kare muradun jama’arta ba? Gwamnati ta al’umma ce, kuma gwamnatin da ta cika gwamnati, ita ce mai sanya al’ummarta gaban komai, wannan ma wani darasi da ya kamata Japan ta dauka daga kasa kamar Sin.

ADVERTISEMENT

Ba al’ummomin wadannan kasashe ba kadai, kuma ba kasar Sin ce kadai take adawa da wannan mataki ba, akwai tarin masana kimiyya da masu rajin kare muhalli da ma tsibiran yankin Fasifik da sauransu, da suka gargadi Japan ta dakatar da kudurin nata, ta kara nazari bisa kimiyya kafin aiwatar da shi, amma sanarwar ta yau, ta nuna cewa Japan ba ta shirya daga kafa ba.

Illar da wannan mataki za ta haifar ga daukacin al’ummar duniya, ya shafe duk wani buri da Japan ke son cimmawa. Haka zalika, Amurka dake ingiza ta, ita ma ba za ta tsira daga mummunar illar da hakan zai haifar ba domin an san cewa, ruwa ba shi da iyaka.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Har yanzu lokaci bai korewa Japan na sauraron al’ummarta da sake nazari domin yin abun da ya dace ba. Kuma ya kamata ta san cewa, baya ga al’ummarta, makwabtanta na da hakki a kanta, kuma Amurka dake ingiza ta, ba za ta kawo mata dauki ba idan abubuwa suka lalace. (Faeza Mustapha)

Japan
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Ba Gaskiya Ba Ne Cewar Muna Kashe Biliyan 196.9 Ga Masu Juna Biyu – Badaru

Harkar Tsaro Za Ta Bunkasa Nan Da Shekara Guda -Badaru

LABARAI MASU NASABA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.