Matar Da Ke Azabtar Da Ƴaƴan Mijinta Ta Shiga Hannun Ƴansand
Rundunar ‘Yansandan Jihar Adamawa ta kama wata mata mai shekaru 37, bisa zargin azabtar da wasu ƙananan yara biyu da take kula da su.
Matar, mazauniyar unguwar Sanda Makama B a ƙaramar hukumar Yola ta Kudu, ana zarginta da dukan yaran da shekarunsu bai kai biyu ba, bisa laifin yin fitsari da bahaya a gadonta.
- Gwamnati Za Ta Samar Da Tsaro A Filayen Hakar Ma’adanai —Alake
- Matsalar ‘Yan sandan Amurka Ta Nuna Karfin Tuwo Na Kara Tsananta
Kakakin rundunar, SP Suleiman Nguroje, ya tabbatar da kama matar, inda ya bayyana cewa mutanen unguwar ne suka kai rahoton ga hukuma dangane da cin zarafin yaran. Makwabta sun bayyana cewa Matar ta saba yi wa yaran wulakanci da kuma hana su abinci, tana kuma gargadin mutane da kada su tsoma baki.
Bayan kama ta, Matar ta amsa laifinta, sannan Kwamishinan ‘Yansanda, Morris Dankombo, ya bada umarnin gurfanar da ita gaban kotu domin fuskantar hukunci.