Jaridar “New York Times” ta kasar Amurka ta ba da labari a kwanan baya cewa, an kai karar wasu ‘yan sanda 5 gaban kotu a jihar Missouri, bisa zargin cin zarafin wani fursuna dan asalin Afrika, matakin da ya haddasa mutuwarsa.
An ce a ranar 8 ga watan Disamban bara, ‘yan sandan sun daure wannan mutum mai suna Othel Moore Jr. mai shekaru 38 a duniya a kujera, aka kulle kan sa da wani kyalle, kuma ‘yan sanda ba su daina cin zarafinsa ba, duk da kokawa da ya yi sau da dama cewa ba ya iya numfashi, har lokacin da ya mutu.
- Xi Jinping Ya Gana Da Vladimir Putin
- Sin Ta Bukaci Isra’ila Ta Sauke Nauyin Dake Wuyanta Dangane Da Samar Da Agajin Jin Kai A Gaza
Lauyan Moore ya ce, wannan abin bakin ciki ya dara abin da ya faru ga George Floyd tsananta. Ya kara da cewa, cibiyar gyara halin fursunoni ta jihar Missouri na da daddaden tarihin cin zarafin fursunoninta, musamman ma kan bakaken fata. Abin da ya bayyana cewa, ba George Floyd da Othel Moore Jr. kadai suka fuskanci irin wannan tashin hankali ba, kuma yadda ake yawan nuna bambancin launin fata a kasar Amurka, da ma yadda ‘yan sandan kasar suke nuna karfin tuwo na da alaka matuka da matsalar.
Shafin yanar gizo na Mapping Police Violence ya ba da kididdiga cewa, a shekarar bara, yawan mutanen da suka mutu sakamkon nuna karfin tuwo da ‘yan sanda suka yi ya kai a kalla 1247, kuma daga cikinsu adadin bakaken fata ya kai kashi 27%, wanda yawansu ya kai kashi 13% kacal cikin dukkan al’ummar Amurka.
Al’amuran irin wannan da bakakken fata suke fuskanta yau da kullum na bayyana cewa, ba a warware matsalar nuna karfin tuwo da ‘yan sanda suke yi ba bayan abin da ya faru ga George Floyd, kuma ra’ayin nuna bambancin launin fata na tsananta halin da bakakken fata ke ciki a wannan fanni. Dole ne gwamnatin Amurka ta kyautata matsayinta, ta dauki matakan da suka dace don magance wannan batu daga tushe, ta yadda za a kare hakkin bil Adam. (Mai zane da rubutu: MINA)