• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matar Da Ta Fi Amfanar Da Al’umma A Shekarar 2024: Olori Atuwatse III

byLeadership Hausa
10 months ago
Olori Atuwatse III

Olori Atuwatse III, ita ce ta kafa gidauniyar Elevate Africa, ta samu wannan karramawar ne saboda gudummawar da take bayarwa ga al’umma ta fuskar amfanar da su a fannonin ilimi da jagoranci nagari da tallafawa jama’a musamman mabuƙata.

Wasu daga cikin ɓangarorin da ta yi fice wanda suka kai ga samun wannan karramawar sun haɗa da tallafawa al’umma ta hannun gidauniyar “Royal Iwere Foundation (RIF)”, Olori, ta samar da shirye-shirye masu tasiri ga jama’a kamar horar da malamai da shirin ƙarfafa gwuiwa a fannin ƙirƙire-ƙirƙire da fannoni da dama wajen mayar da hankali a fannin inganta ilimi da kiwon lafiya da inganta tattalin arziƙi ga matasa, musamman ‘ya’ya mata da  sauran al’umma.

  • Katafaren Aikin Karkatar Da Ruwa Na Sin Ya Karkata Kyubik Mita Biliyan 76.5 Zuwa Arewacin Kasar
  • Bankin Zenith Ya Tallafa Wa Matasa Da Naira Miliyan 77 A Jihar Legas

Ta kasance mamba a babban kwamitin bayar da shawarwari kan inganta harkokin mata a Nijeriya (HLAC), don bai wa mata damar dogaro a kai. Olori, ta haɗa kai da gwamnati a fafutukar da take na magance matsalolin da suka shafi mata da kawar da fifiko wajen samar da damarmaki.

Olori Atuwatse III, tana matuƙar ƙoƙari wajen ganin ci gaban matasa ta yadda take taka muhimmiyar rawa don  samar wa matasan kayan aiki da ba su horo kan fasahar sana’o’i ta yadda za su dogara da kansu, wannan yunƙuri ya taimaka wajen kawar da zaman kashe wando a ƙasarnan, tare da bai wa matasa damar yin nasara wajen cimma burikansu na rayuwa.

Olori, mace ce mai matuƙar tasiri a duniya, kasancewarta ɗaya daga cikin Matan Afirka 100 masu tasiri a shekarar 2023, ta kuma taɓa yin alƙalanci a shirin gasar lambar yabo ta Diana a 2024, bugu da ƙari tana taka muhimmiyar rawa a matsayin mai bayar da shawara don samar da  ingantaccen canji a duniya.

LABARAI MASU NASABA

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

Baya da cewa ta yi karatu a fannin shari’a daga Makarantar Tattalin Arziki ta London, Olori, ta kafa manyan wuraren harkokin kasuwanci da yin nasara a ɓangarori daban-daban da suka haɗa da fannin dinke-dinke da sauransu, ta kuma kasance ɗaya daga cikin masu jagorantar masana’antu da dama, inda ta bayar da bayar da gagarumar gudummawa wajen  ɓunƙasa su.

Olori Atuwatse III, ta yi gadon mulki da tasiri a wajen al’umma, kasancewarta Sarauniyar Warri, kuma uwa ce mai kishin ƙasa wadda ta himmatu wajen barin gadon ilimi da ƙarfafa wa al’umma da samar musu da ci gaba mai ɗorewa a masarautar Warri da duniya baki ɗaya.

Olori Atuwatse III, mata ce ga Sarkin Warri Ogiame Atuwatse III, wanda suke da ‘ya’ya uku, rashin nasara ba ya daƙile mutum wajene cinma burinsa, sai dai ta haska masa ba ya kan turbar da zai kai ga nasarar da inda ya kamata ya bi. saboda haka akwai buƙatar ya sauya alkibla tare da ƙara ƙaimi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Labarai

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa
Labarai

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Next Post
Bamanga Usman Jada

Gwarzon Shugaban Kamfani Mallakar Gwamnati Na 2024: Bamanga Usman Jada

LABARAI MASU NASABA

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version