Wata dattijuwa da ta fi tsufa a duniya ta mutu tana da shekaru 118 a birnin Toulon da ke yankin yammacin Faransa kamar yadda magajin garin ya sanar a hukumance.
Tsohuwar mai suna Lucile Randon ta kasance malamar majami’a a ranar 11 ga watan Fabrairun 1904, an sanya sunanta a cikin jerin mutane mafiya tsufa a duniya a cikin watan Afrilun 2022.
Bafaranshiyar ta yi aiki a matsayin malama mai koyarwa a gida a lokacin da take matashiya, wato gabanin ta mayar da hankali kacokan kan hidimar addini tana tsakan-kanin shekaru 40.
Gabanin mutuwarta, marigayiyar ta yi fama da larurar makanta, sannan ta ci gaba da rayuwa a kan kujerar marasa lafiya.
A shekarar 1944 ne, Randon ta sauya sunanta zuwa Sister Andre, yayin da kundin adana tarihi na duniya, Guiness Book of Record ya bayyana ta a matsayin ta biyu mafi tsufa a cikin al’ummar Faransawa da yankin Turai baki daya da aka taba gani a duniya.
Rfi HausaÂ