Allah ya yi wa matar fitaccen Farfesan harkar shari’ar nan, Farfesa Auwalu Yadudu, Hajiya Zainab Auwalu Yadudu rasuwa a Kasar Amurka, bayan ta sha fama da jinya.
Farfesan, wanda tsohon shugaban sashen nazarin shari’a ne na Jami’ar Bayero Kano, ya aike da sako, inda ya ce ta rasu ne a Amurka a yammacin ranar Lahadi.
Ya ce sun kwashe sama da shekara 40 tare, kuma ta rasu ne a asibiti bayan ta cika kalmar Shahada, inda ya kara da cewa ana shirin kawo gawarta Nijeriya domin yi mata jana’iza.
“Allahu Akbar, yanzu na samu sako daga Farfesa Auwalu Yadudu daga Kasar Amurka, inda ya bayyana bakin cikin rasuwar matarsa da suka shafe sama da shekara 40.
“Daga Allah muke kuma gare shi za mu koma. AlhamduliLlah, Zainab Auwalu ta rasu da kalmar Shahada a bakinta a yau 8 ga watan Janairu 2023 a asibitin Jami’ar Kentucky da ke Kasar Amurka da misalin karfe 12:52 na rana.”
Farfesa ya ce yanzu haka sun kammala shirin dawo da ita gida Nijeriya don yi mata sutura kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar.