Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriya Dauda Lawal, ta ɗauki nauyin tantancewa da yi wa mata dari masu ɗauke da cutar kansar Nono tiyata kyauta a fadin jihar ta Zamfara.
Hajiya Huriyya ta bayyana hakan ne A yau Litinin yayin bikin tunawa da ranar mama ta duniya ta 2024 a jihar.
- Matsalar Tsaro: Gwamnonin Zamfara Da Katsina Sun Gana Da Ministan Tsaro Da Ribaɗu
- Ɗaliban Cyprus: Zamfara Ta Samar Wa Ɗalibanta ‘Yanci Da Ke Karatu A Gida Da Ƙetare
A jawabin ta ta bayyana cewa,
yau ne ranar yaƙi da kansar Nono ta duniya don haka mu kabi sahu wajan tallafawa Mata masu ɗauke da wannan cuta mai haɗari da ke jawo asara rayuka a Jihar mu.
Uwargidan Gwamnan ta ci gaba da cewa
tare da goyon bayan maigidana gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal, an tantance majinyata 100 da suka kamu da cutar kansar Nono za a yi musu aikin tiyata kyauta a jihar.
A kan haka muke kira ga waɗanda za a yi wa aikin da su bi dokar likitoci a lokacin jinyar don samun nasarar aikin da ɗorewar lafiyarsu.