A jiya Lahadi ne mai martaba Sarkin Jama’are, Alhaji Nuhu Muhammadu Wabi ya nada matar tsohon shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa a karkashin Muhammadu Buhari, marigayi Abba Kyari, Hajiya Hauwa Kulu Abba Kyari a matsayin ‘Gimbiyar Masarautar Jama’are’ ta farko.
Da ya ke jawabi a wajen wankan sarautar a fadarsa, Sarkin Jama’are, Nuhu Muhammadu Wabi ya misalta Hajiya Hauwa Kulu a matsayin diya ta kwarai ga masarautar wacce ta bada gagarumin gudunmawarta wajen bunkasawa da inganta cigaban masarautar Jama’are.
A cewar Sarkin, Girmbiyar za ta taimaka sosai wajen kara kusanto da mata su samu hanyoyin magana kai tsaye da masarautar domin tabbatar da ci gaba mai ma’ana, “Da wannan nadin na Gimbiyar Jama’are ta farko, yanzu matan Jama’are sun samu wakilci a cikin masarautar kuma za a ke jin muryoyinsu.”
Ya ce cikin farin ciki a yanzu yana da diya ta kwarai a cikin Majalisar masarautar Jama’are. Jajircewa mace ce wacce ta damu da maida hankali kan cigaba kuma ta bada gagarumar gudunmawa wajen cigaban masarautar Jama’are.
Sarkin ya kara da cewa, “Bisa irin rawar da ta taka wajen cigaban masarautar Jama’are da ma wadanda take kan yi, suka sa muka nata Gimbiyar masarautar nan. Don haka muna fatan wasu gudunmawar daga gareta yanzu da nauyi ya karu a kafadunta”.
A dan gajeren jawabinta bayan nadin, Gimbiyar masarautar Jama’are ta farko, Hauwa Kulu Abba Kyari ta gode wa Sarkin bisa wannan karamcin da ya mata da ya zo mata a matsayin bazata.
Ta jaddada aniyarta na kara bada gagarumin gudunmawa domin cigaban masarautar Jama’are da al’ummar masarautar baki daya.
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan nadin, babban Manajan gudanarwa na NNPC, Mele Abba Kyari, ya nuna fatan alkairi ga Gimbiyar Jama’are ta farko, ya nuna fatansa na cewa wannan nadin zai karfafa guiwarta wajen cigaba da taimaka wa masarautar da jama’an Jama’are baki daya.