Assalamu Alaikum Warahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu.
Jama’a barkanku da kasancewa tare da wannan fili mai albarka, filin da nake kawo muku batutuwan da suke ci mun tuwo a kwarya, wanda a yau ma ina tafe da wani batun wanda nake son jan hankali akai musamman ga maza.
 Idan muka yi duba da yanayin da muke ciki na rayuwarmu, musamman a arewacin Nageriya ko na ce Hausawanmu, za mu ga yadda rayuwar Malan bahaushe ke tafiya a yanzu, misali; mutum ne yake a gidan haya, yanada mata guda daya, da kuma yaronsa daya ko biyu, ya kan dan biya musu kudin makaranta a hankali, wal’alla ya samu dan dama ya siyi babur din hawa ko makamancin hakan cikin rufin asiri, ya kan dan ci da su da safe, rana, da kuma dare, har cikin ikon Allah za a ga ya dan samu abin da za a kai baki na kwadayi da sauransu.
Sai dai wata dabi’a irin ta Malan Bahaushe wadda take zama tushen matsala a zamantakewar rayuwa, duk da kasancewarsa cikin irin wannan hali, hakan baya iya hana shi yawan aure-aure. Da zarar ya dan samu wasu dan kudin saman kudin da yake samu, madadin ya tsaya ya tsarawa kansa rayuwa ta yadda zai taimaki kansa da kuma iyalinsa, kan abin da zai amfane su a gaba kamar dai; Gina gida, Siyan fili, ko canja sana’a me gwabi, ko kara jari, ko makamancin haka, amma ina! sai ya je ya kara aure, wanda hakan yana daya daga cikin abubuwan da suke janyo tabarbarewar zamantakewar aure, har ta kai ga an samu matsala a tsakanin iyali.
Sai dai wani hanzari ba gudu ba, na kan rasa gane irin wannan hali na Malan Bahaushe game da yawan aure-aure, wai shin hakan dabi’a ce ko kuwa gasa ce?
Mu yi hakuri mana saurin me muke yi?, ya kamata a kiyaye, kuma ayi adalci, idan ka san ba za ka iya yin adalci ba to, kayi hakuri da matarka guda daya da ‘ya’yanka.
Ya kamata a rinka sara ana duban bakin gatari, ta yadda idan aka ga wani ya yi mata uku wal’alla yanada wadatar da zai yi mata ukunne, madadin ace kana gidan haya ka auri mace daya, ka auri biyu, kayi ta uku, kuma kana harin ta hudu, shin me yake damunka?
Yanada kyau iyayen da suke bayar da ‘ya’yansu aure, su rinka yin hakuri wajen yin buncike da kyau, idan suka tabbatar da mutum zai auri ‘yarsu yanada mata biyu duk a gidan haya to, bai kamata a bashi auren ba duk rufin asirinsa. Ba dan komai ba, sai dan gudun abun da yake juyawa ya zamo ba nasa ba, wannan zalama ce da kuma hadama.
Haka ma matan da suka tsinci kansu a irin wannan yanayin, su yi hakuri, muddin mijin yana iya sauke nauyin matar da Allah ya dora masa a kanshi to, ta zauna, kada a zugata ta fita. Tunda in ma ta fita ba a san inda za ta je ba, ina kuma kara kira ga ‘yan uwana maza cewar; dan Allah mu rinka yin hakuri, auren nan fa ba dole sai ka yi biyu ko uku ba, matarka daya ta ishe ka, biyun fa cewa aka yi idan za ka yi adalci, uku sai za ka yi adalci, hudu sai za ka yi adalci, daya ce aka ce maka ka yi.
Da wannan nake kara jan hankali cewa; dan Allah kodan zaman lafiyarmu da iyalanmu da ‘ya’yanmu, saboda baka san inda ‘ya’yanka za su je ba, sai ka ga mutum ya je ya haifi ‘ya’ya kusan goma sha, matamsa kowacce gidanta daban-daban haya ake biya, ina dalilin irin wannan?
Mu yi wa kanmu fada mana, mu tsaya mu tsarawa kanmu rayuwar da ba za mu sha wahala ba.
Wassalamu Alaikum.