Rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi, ta kama wasu matasa huÉ—u da ake zargi da garkuwa da kuma kashe wani yaro mai shekara shida, Shuaibu Safiyanu, a Æ™auyen Sade da ke Ƙaramar Hukumar Darazo.
LEADERSHIP Hausa ta samu rahoto cewa mahaifin yaron, Safiyanu Abdullahi, ya kai ƙorafin ɓatan ɗansa ga Sarkin garinsu, Musa Isah, a ranar 20 ga watan Maris, 2025.
- Dalilan Gwamnatin Tarayya Na Zuba Naira Tiriliyan 1.5 A Bankin Aikin Noma -Kyari
- Chelle Ya Fara Da Ƙafar Dama A Super Eagles
Washegari, mahaifin yaron ya samu kiran waya daga wani mutum da bai sani ba, yana neman kuÉ—in fansa.
A farko ya nemi miliyan uku (₦3,000,000), daga bisani aka rage zuwa Naira dubu ɗari biyu (₦200,000).
Sai dai a ranar 21 ga watan Maris, an gano gawar yaron a cikin daji, an É—aure masa wuya da igiya.
Likitoci sun tabbatar da mutuwarsa, daga nan aka bai wa iyalansa gawarsa domin yin jana’iza.
Kakakin ‘yansandan Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce suna samun labarin lamarin, jami’ansu suka fara bincike, musamman a wajen POS da ke kusa da inda aka nemi a biya kuÉ—in fansar.
A yayin binciken, sun kama wani matashi mai shekara 23, Rabi’u Muhammadu daga ƙauyen Leka, wanda lambar wayarsa aka yi amfani da ita wajen kira mahaifin yaron.
Sun kuma gano asusun bankin da aka bayar don a biya kuÉ—in fansar.
Da aka tambayi Rabi’u, ya bayyana cewa Samson Ozoichikel, mai shekara 35 daga ƙauyen Sade, shi ne ya shirya yin garkuwa da yaron.
Sannan ya ambaci wasu matasa biyu, Muhammad Sani (Jingi) mai shekara 25 da Musa Usman (Kala) mai shekara 30, dukkaninsu daga ƙauyen Leka.
A halin yanzu, ‘yansanda sun tsare waÉ—anda ake zargi, kuma ana zurfafa bincike a sashen manyan laifuka (SCID).
Kwamishinan ‘yansandan Bauchi ya tabbatar da cewa za su yi duk mai yiwuwa domin ganin an yi adalci.
Ya kuma roÆ™i jama’a da su ci gaba da bai wa rundunar haÉ—in kai da kuma sanar da ‘yansanda duk wani abu da suke zargi a layin gaggawa na 112 ko Police Control Room a lamba 08156814656.
Rundunar ‘yansandan Bauchi ta jaddada cewa tana nan daram domin kare rayuka da dukiyar al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp